Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta'aziya Ga Iyalan Sojoji Da Al'ummar Garin Mutunji Kan  Rasa Rayukka Sakamakon Farmakin 'Yan Bindiga

Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta'aziya Ga Iyalan Sojoji Da Al'ummar Garin Mutunji Kan  Rasa Rayukka Sakamakon Farmakin 'Yan Bindiga
 

Daga Hussaini Ibrahim

 

Gwamnan jihar Zamfara,Hon Bello Matawalen Maradun ya mika ta aziyarsa ga iyalan Sojoji da al'ummar garin Mutunji a karamar hukumar Maru  da suka rasa rayukan su Sakamakon farmakin 'yan bindiga da  Sojojin sama suka yi a yankin.

 
Matawalen Maradun ya bayyana haka ne a taron da yayi da manema labarai a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
 
A jawabinsa, Matawalen Maradun ya jinjinama dakarun Sojojin da suka sadaukar da rayukansu wajan kare al'umma har Allah ya sa sandiyar haka ne suka rasa rayukan su.dan fatan Allah ya gafarta masu ya albarkaci abunda suka bari amin.
 
Suma al'ummar garin Mutunji da sandiyar harin ya sanya suka rasa rayukan su suma Allah ya jikan su ya albarkaci abunda suka bari.
 
Gwamna Matawale ya kuma tabbatar da tallafawa iyalan Sojojin da al'ummar garin Mutunji da suka rasa rayukan su da kuma daukar nauyin wadanda suka samu munanan raunuka da suke kwance a Asibiti yanzu haka.
 
Gwamna Matawale ya kuma tabbatar da cewa,Lugudan wuta ga 'Yan ta'adda yanzu aka fara da yardar Allah sai mun kakkabe su daga cikin wannan yanki namu Insha Allah.
 
Ya kuma yi kira ga al'ummar dasu cigaba da bayyana mafakar 'yan ta'adda a duk inda suke a fadin Jihar ta Zamfara,dan kawo karshen su.