WATA UNGUWA: Fita Ta 32

WATA UNGUWA: Fita Ta 32

BABI NA TALATIN DA BIYU

 

Bayan ficewar Sofi daga office ɗin da kamar sa'a biyu, wanda Irfan ya tura don yo masa bincike akan Jafsee ya dawo.

Bayan sun gaisa ya ce

     "Ranka Ya daɗe na samo wasu muhimman bayanai dangane da wannan yaron Ja'afar.

 Ainahinsa ba mazauni wannan unguwar ba ne, gidan iyayensa yana unguwar Bashal. bariki ce ta zaunar da shi a unguwar Dagarman, wani Gaye na samu a cikin abokanan shiriritar tasa shi ne ya yi mini bayanin komai, har ma ya nuna mini hoton Ja'afar ɗin.

    A taƙaice dai ranka ya daɗe na zauna a ƙofar wannan gidan har zuwa lokacin da Jafsee ya fito don zuwa gidansu kuma na bi bayansa na gano har gidan nasu."

 

Irfan ya ɗaga hannu cikin alamun jinjinawa ya ce

   "Well done, ka yi ƙoƙari sosai. Yanzu ka zo mu je ka nuna mini gidan iyayensa da kuma shi yaron."

 

Ya yi saurin ɗaga kai ya kalli Irfan kamar zai yi magana kuma ya yi shiru.

Irfan ya gyaɗa masa kai tare da faɗar

    "Ƙwarai can za mu je kuma yanzun nan, ai ba a bori da sanyin jiki. Baka ji 'yan magana sun ce da zafi-zafi akan daki ƙarfe ba?"

 

Mutumin ya yi murmushi, bisa ga tilas ya bi bayan ogan nasa ya kai shi inda ya buƙata.

 

Koda suka ƙarasa ƙofar gidan ana kiraye-kirayen sallar azahar. Kafin Irfan ya gama daidaita tsayuwar ƙafafun motarsa ya ga fitowar wani Dattijo daga gidan yana sauri.

Daga damshin ruwan da ya gano a fuska da hannuwan dattijon ya fahimci Masallaci ya nufa. Don haka cikin hanzari ya fito daga motar ya ƙarasa wurinsa suka gaisa.

      "Baba idan ba damuwa ina son yin magana da kai."

 

"Shi kenan yaro bari na fito daga masallaci." A tare suka ƙarasa masallacin su Uku. Bayan sun idar da sallah ne suka dawo ƙofar gidan tare da tsayawa.

 

Cike da fara'a malam Rabe ya ce "Yaro ina saurarenka."

 

Irfan ya yi murmushi yana kallon dattijon mai cikar kamala.

"Don Allah Baba kai ne Mahaifin Jafsee?"

 

Dattijon ya masa wani irin kallo alamun rashin fahimta a take ya ɗago kuskurensa

 

"Am! Ja'afar nake nufi Baba."

 

Dattijon ya Ƙawata fuskarsa da murmushi.

"Ƙwarai kuwa Jafaru ɗana ne da nake ji har tsakiyar rai saboda tarbiyyarsa."

 

Irfan ya yi busasshen murmushi a ransa ya ce

 

   _'Da alama ya gama yaudare zuciyar salihan iyayensa sun kasa fahimtar cewa kura ce lullube da fatar akuya.'_

 

"Ina jinka yaro, kai abokin Jafaru ne?"

 

'Allah ya tsari gatarina da saran shuka.' Irfan ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kuwa cewa ya yi

 

"Am, wata magana ce tafe da ni wacce zaka iya jinta tamkar almara, sai dai kuma ba almarar ba ce. Ja'afar ya yi mana wani gagarumin laifin da za mu iya maka shi a kotu idan mun so, amma kamalarka da ƙimarka da na duba shi ne na fara zuwa gare ka don a yiwa tufkar hanci."

 

Malam Rabe ya ɗan razana kaɗan

     "Me kake nufi yaro? Shi Jafarun?"

 Ya shiga girgiza kai yana faɗar

    "Ina! Sai dai ko in ɓatan kai ka yi."

 

"Ba ɓatan kai ba ne Baba, Ja'afar ɗinka wato Jafsee shi ne wanda ya lalata rayuwar ƙanwata, kuma matar da nake burin aura, yanzu haka ba mu san inda za a same ta ba, kuma shi nake zargi da sace ta."

 

Shuu! Wutar lantarki dake aiki a jikin malam Rabe ta ɗauke na wucin gadi, ya ƙame tamkar mutum-mutumi kafin daga bisani ya samu damar motsa harshensa.

 

      "Yaro ina yi maka kallon mai kamala duba da shigar da ke jikinka da kuma nutsuwarka ashe dai kai motsattse ne?, wannan abin da kake faɗa abin da ba zai yiwu ba ne auren mage da ɓera."

 

Yana gama rufe bakinsa ya hango tahowar Ja'afar riƙe da  baƙar leda a hannu da alama cefane ya yo.

 

Dattijon ya yi murmushi "Ai shi kenan inda ba ƙasa ake gardamar kokowa, ga Jafarun nan zuwa, zaka tabbatar da cewa ka yi ɓatan kai ne."

 

Irfan ya yi saurin juyawa ya kalli bayansa ya hango mai tahowar, a take ya ji wani ƙololon baƙinciki ya tokare masa maƙoshi.

 

      'Wai wannan abun ma shi ne Jafsee? Wannan ƙazamiyar halittar ce Mahee ta guje ni saboda ita? To me ta gani a nan? Wannan gajeren hancin ko kuwa ƙaramin kan nan nasa mai kama da na jinjirin jaki?'.

 

 ya fara nisa a duniyar tunani ya tsinto muryar Ja'afar ɗin yana faɗar

      "Barka da rana Abba, Ɓaki sannunku da zuwa."

 

Abban nasa ya faɗaɗa murmurshinsa "yawwa ɗan albarka da ma a kanka muke magana da yake kai ɗan halas ne sai ga ka."

 

Ya juya ga Irfan "Ɗan samari maimaita tuhumarka ya ji."

 

Jafsee ya tsaya yana rarraba ido       "Tuhuma kuma Abba? Ni Jafaru me na yi musu kuwa?"

 

Abban nasa ya ce "Wannan ne ya ce ka lalata masa rayuwar ƙanwa kuma yana tuhumarka da sace ta."

 

Dam! dam!! ƙirjinsa ya buga a zuciyarsa ya ce

      'Wata sabuwa inji 'yan caca, wannan kuma yayan wace jakar ne a cikin Jakunan...'

 kafin ya ƙarasa zancen zucinsa ya jiyo sautin matashin yana cewa.

 

"Ƙanwata Maheerah wacce ka yaudare ta a watannin baya, ka koya mata shaye-shaye kuma ka raba ta da mutuncinta, kuma kai nake zargi da ɓoye ta ko ince sace ta."

 

"Daram dam!" Sautin bugawar ƙirjin Ja'afar kenan, A take 'yan hanjinsa suka shiga ƙadawa tare da ba da wani sauti ƙululu-lu. Da ace mutanen da ke wajen sun ajiye hankulansu a gun da za su iya jiyo sautin kaɗawar hanjin nasa."

 

'Wannan fa shi ne an yanka ta tashi, Maheerar da tuni na manta da babin rayuwar ta ga shi tana neman jefa ni a masifa tare da barazanar raba ni da albarkar iyaye....' 

Ummu Inteesar ce