HAƊIN  ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Takwas 

HAƊIN  ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Takwas 
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
 
 
 
 
 
*INNALILLAHI WA INNA'ILAIHIRRAJI'UN!!!*
 
Allah Ya yiwa magajin mahaifiyata (Yayan Mamata) rasuwa a yau Alhamis(data gabata), ina neman addu'arku Allah Ya jiƙansa Ya gafarta masa Yasa ya huta. Mahaifiyata ma bata lafiya ina neman addu'arku Allah Ya bata lafiya Yasa kaffarane tare da sauran marassa lafiya na gida dana asibiti.
 
Haupha..........
 
 
       Page 18
 
Haka nake tsugunne har asuba sannan na dawo daidai, na tashi da ƙyar na ɗauke Haidar dake kwance ƙasa, na sashi ya yi fitsari na kwantar da shi, jin ana kiran sallah yasa nayi alwala na kabbara sallah, na gama na fara lazumi naji barci mai nauyi ya kamani, don haka na rungume Haidar barci ya ɗauke Ni.
Can cikin barci naji kukan Haidar, na buɗe idona da ƙyar, naga gari ya waye tangaram, don haka na tashi don nasan kukan yunwa yake, sauran abincin jiya na duba bai yi komai ba, don haka na hura wuta na ɗumama shi, na zuba ma Haidar, na shiga wanka na fito na ci nawa, shi ma nayi mai wanka.
Sai naji a raina ya kamata na je gidansu Abban Haidar na gano shi, ba wai don ina jin ban kyauta ba na dukan da nai mai ba, sai dan da daɗi yana mijina ya kwana wani waje na je naga yadda ya kwana.
Na shirya tsab zan fice kenan wata abokiyar wasana ta iso ƙofar gidan, don haka na fasa rufewa muka shiga cikin gidan.
Bayan ta zauna ta fara tsokana ta, "Sai ina kuma iyayen yawo? Ke dai kullum kamar kin ci ƙafar Kare ba a iske ki gidanki, ko dai mijin ke korarki?"  Ni dai murmushi kawai nake, don ban iya wasan da ake kira na tsakanin ɗan mace da ɗan namiji ba.
Can ta nisa tace min, "Jiddah ina tason na ganki mu yi magana amma Allah bai sa mun haɗu ba, kuma nayi alƙawarin idan ba ke na gani ra'ayil ainu ba, cikin gidan nan ni da gidanki har abada. Na dube ta da fuskar mamaki, harma da tambaya. Tai ajiyar zuciya tace, "Jiddah kwanakin baya can na zo zan wuce ta unguwar nan, sai na hango gidanki sai nace a raina bari na shigo Mu gaisa, tun da ke baki iya zuwa gidan mutane, gidan Inna (Mamana)kawai kike zuwa ko kin je wajajen mu. Ina shigowa gidan nan da sallamata na iske maigidan, ya leƙo daga ɗaki yace, "Ki shigo man kin tsaya tsakar gida?" Ni kuma ina dariya nace, "Ina ƴar ƙauyen matarka ta fito ta kawo gaisuwa na zo." Yana ƴar dariya yace, "Shigo ki zauna man sai ta baki amsa ai tana da bakinta." Nace nima ina dariyar "Kai haba yaushe tai bakin ban da labari? Ai Ƙura ce matarka tsoron mutane take balle ta iya maida masu magana." Ina maganar na shiga ɗakin na zauna. Ya  dube ni yace, "Yanzu ta ɗan fita nan makwabta yanzu kin ganta ta dawo ina ga ko magi taje siye." Da yace hakan sai na zauna ina jiranki, tunda yace kina kusa. Jiddah ina zaune kan kujerar can mai zaman mutum biyu ban san ya akai ba kawai naga Deeni zaune gab da Ni, yana ta murmushi yace, "Wallahi ina ta son dama na je gunki mu yi wata magana ban samu damar zuwa ba...yana magana yana neman ɗora hannunsa kan ƙirjina. Na yi Wuf na miƙe tsaye ina zare idanuwa gabana na faɗuwa. Sai yace mun "Ke wasa nake maki bata ma kusa tana gidanmu kawai ki saki jikinki... Ban bari ya ida ba na nufi ƙofa amma dai ya yi sauri ya isa gun ƙofar ya rufe ta. Mu kaita yawo cikin falon nan dole sai ya taɓa min ƙirji Ni kuma na ƙi, muna ta yawon nan Allah Ya gwadamin rediyo na kuwa ɗauka ciccin ƙarfina na maka mai ita, ya duƙe ta faɗi kafin ya ankara na fice da gudun tsiya ina zaginsa ta Uwa ta Uba. Ke Jiddah ranar naga ikon Allah! Kamar bai san Ni ɗin ƴar'uwarki bace ba? Kuma nasan dai ai yasan sai na gaya maki, tunda ke ɗin jinina ce." 
Ajiyar zuciya nayi, bakina ya yi min nauyi, tabbas Abban Haidar do yake ta kowane ɓangare sai ya zubar min da mutunci, wane irin abu ne wannan ka nemi ƴar'uwar matar da fasiƙanci? Cike da jin kunyar abun na dube ta nace, "Don Allah ki yi haƙuri, ban san kuma ki gayama kowa, don Allah maganar ta tsaya iyakar Ni da ke, don Allah." Tai min kallon tausayi tace, "Jiddah daman kin san halinsa haka ye? Daman kin san ɗan iska ne Deeni? Gaskiyar magana kin ban mamaki ko ni da ban aure ba wallahi babu ɗan iskan mijin da zai dinga kawo min mata cikin gida kuma ina sane na ƙyale shi. Idan gani kike wani abin kirki ne to wallahi ba komai bane illa sakarci da mai da kai baya, sannan idan ma don yace kina da kirki ko babu ruwanki ko ya kira ki da macen kirki kin makaro, wallahi yanzu wasu mazan ba ai masu haka, sai kin tashi tsaye kan shi kina nuna mai kin san ciwon kanki, sannan za ki iya ɗaukar kowane mataki kan shi idan bai bar halayensa ba. Yo Allah na tuba Jiddah wannan zamanin wace sakaryar mace ce zata amince da wannan iskancin na mijinki? Shike nan ke baki da wani ƴanci balle martaba ko kimar da zasu sa Deeni dinga kiyaye ɓacin ranki?" 
Tun da ta fara magana hawaye suke zubowa daga idona, ban san me zan ce mata, har ma da sauran mutanen da ke min kallon Sakarya ba, shin ya zan da halin Deeni ni? Duka nawa nake? Me nasani ma kan rayuwar auren na jin daɗi? Ban da yadda zan Deeni, shi ɗin halinsa ko da yaushe ƙara gaba yake madadin baya, da farko na ɗauka idan na haihu yana ganin abin da na haifa zai natsu ya daina abin da yake, ko dan kar watarana ai ma shi gori ko yaron yaga abin da bai kamata ba daga gare shi, ko jin mummunan labari akan rayuwarsa... "Au wai kuka na saki daga gaya maki gaskiya? Anya kuwa Jiddah kin san ciwon kanki yadda ya kamata kuwa? Kai ban zaton kin san wacece mace kawai sunan macen gareki baki da halayenta kam gaskiya. Ta miƙe tsaye"To ni kinga tafiya ta, ruwanki ne ki gyara haka ruwanki ne ki bari yana maki cin kashi kina kuka, shi kuma abin murna ya same shi tunda ya ga hawayenki." 
Har ta fice daga gidan ban tanka mata ba, don babu abin da zan iya ce mata Ni kam. Bayan ta tafi na miƙe na ɗauko rediyon tabbas batai ƙarya ba, don ga rediyon nan ta fashe, haka zalika idan zan faɗi gaskiya ya jima bai kunna ta sai da naga ya kwance ta yana gyara,ashe abin da ya faru kenan? To Allah Ya shirya shi Yasa ya gane gaskiya-gaskiya ce. Ganin rana ta kawo kai nasan ba lallai bane na je a ban abinci ko a ba Yarona ba yadda mutanen gidan ke fusace dani kan abin da Ni a ganina ban laifi ba, yasa na tashi na nemi abin da zan ci Ni da Yarona, duk da wata zuciyar na raya min na dafa abincin da yawa na kai mai gidansu, amma ina gudun ya ɗauka ina ma da kuɗi ko abincin da yawa ya ƙi ban, ga shi abincin ba shi ne da Ni ba, kawai ƴan dabaru ne nake ina dafa mana abin da ya sawwaƙa muna ci.
 
Hakan yasa sai yamma na fice na nufi gidansu, jama'ar unguwa nata min ya mai jiki, duk da nasan gulma ce tasa suke tambayata haka na share nake amsawa, marassa kunyar ciki har tambaya ta suke ko can zan je nema gunsa? Wasu kuwa tambaya ta suke amma yana asibiti ko? Duk ban da amsar basu irin su, sai dai na wuce kawai ban tanka masu.
 
Ina zuwa na iske jama'ar gidan kowa nata hidimarsa, ban damu da yadda sukai tsit da maganar da suke ba,wadda tun a zaure na gama fahimtar shawara suke ba shi kan zamana da shi, kar ya kuskura ya sake haɗa jiki da Ni wai zan iya sabauta shi fiye da hakan, ko ma na kashe shi, duk iskancin da zan ma shi ya je gun uwata tunda nafi jin maganarta ya gaya mata, ta ɗauki mataki, amma kar da ya kuskura na sake bugunshi irin haka a banza.
Tun a zauren na taɓe bakina don wannan su ta shafa, tsorona guda ya je ya ja min sharri gun Mama, ban san abin da ranta zai ɓaci sam a kaina.
 
A hankali na dinga gaishe su, suna amsawa tamkar basu so. Na samu waje na zauna Ni da Yarona, muka bi sahun ƴan jinya tun da na lura jinyar ake ka'in da ka'in ba kama hannun yaro, har da su lemu da ayaba a gabansa. 
Yau ma bai tanka min ba, haka bai tankawa Haidar ba, duk da naji ba daɗi amma na cije don ba yadda zan yi.
 
Ganin ina ta zaman banza, na tashi na tattara kayan wanke-wanke nayi na gama na yi shara, ina gamawa ana kiran sallar magrib, na yi sallah na zauna nan ina ta lazumi har ishsha'i nayi ta, lokacin, Haidar ya gaji da kukan yunwa ya yi barci kusa dani.
 
Yau ma kamar wadda aka riƙe sai da kowa ya yi barci sannan na goya Haidar na nufi gida.
Yana tsaye da fitilarsa mai haskeb gaske mutumin jiya, Yau ma kamar jiya ban ga kansa ba, ya yi gaba ina bayansa yana haska fitilar hannunsa. Haka muka tafi har ƙofar gidana na buɗe yana tsaye na shige na maido ƙofar na rufe, na je na buɗe ɗakin na shige. Yau ma kamar jiya ina shiga ɗakin tsoro ya kama Ni sosai, da ƙyar na kwance Haidar dake bayana na ƙudundune waje guda.
Sai asuba na samu natsuwa nayi sallah na kwanta barci mai nauyi ya ɗauke Ni.
 
Da rana ina zaune ina tunanin me zan dafa mana ban da komai ga Haidar sai kuka yake, na buɗe gidan na fita naje gidan Binta ta ara min kuɗi ko fura na sai ma Haidar nasan kukan yunwa yake .
Ta kuwa ban aron Naira ɗari, bayan na dawo ta zubo abinci mai yawan gaske ta bada aka kawo min lokacin ina dama furar da na siyo.
Gama cin abincin ke da wuya Haidar nata wasansa Safiya tai sallama gidan.  Na amsa mata ina daga inda nake zaune... Ko shigowa bata ida yi ba ta fara maganar "Yanzu ke Jiddah kin kyauta wa rayuwarki dukan miji? Tun da nake ban taɓa jin labari ko ganin wadda ta bugi miji har ta tsugunnar da shi ba sai ke." Na dube ta nace, "Zagina ya yi fa, kuma don na rama ya mare ni."  Ta dube ni cike da haushi tace, "To dama duk mace ai bata wuce duka da zagi gun mijinta ba, ko sai ke shafaffa da mai? Jiddah ban san ki da wannan mugun halin ba sam, kuma nasan dai ba kishin Deeni kike ba balle ki ce kishi ne yasa ki kai mai haka ba. Nafi kowa sanin cewa baki son Deeni domin ba shi ne burin ki ba, kawai kin auri Deeni ne don zaɓin iyayenki ba wai zaɓin zuciyarki ba. Don haka yasa ban damu da alaƙar dake tsakanina da shi ba Jiddah... Kawai kaina naji na juyawa ban san ya akai ba sai buɗe idona nayi naga mutane kewaye da Ni, sun yi tsuru-tsuru ga wani uban ƙauri daya turnuke ɗakin baki ɗaya. 
 
"Yawwa ta dawo hayyacinta, ita ce yanzu." Abin da naji ana cewa kenan, kaina ke ciwo sosai don haka na rufe idona ina jin kukan Haidar na tashi amma ban iya buɗe idona don azabar ciwon da yake min. Sannu kawai ake jera min. Ina jinsu amma bakina ya datse ban iya amsawa sai dai a cikin zuciyata nake amsawa. Mutane sun jima zaune suna ta min sannu amma abin mamakin bakina sam bai buɗewa, dole na haƙura kawai nayi lamo har barci yak kwashe ni. Ban farka ba sai can na tashi naga ba kowa sai wata Maman Khairat zaune tana cin abinci Haidar na zaune shima yana cin abincin. "Kin tashi? Sannu tashi ki kuskure bakinki ki ci abinci. Maman Kahairat can ƙasan layinmu take saboda ansar aron littafin Hausa na santa ta sanni. Na miƙe jikina sanyi ƙalau kamar an mun duka na tashi ina cije baki na kuskure bakina ta miƙo min shinkafa da miya har da nama, na amsa na ci iyakar ci na ta ban ruwa na sha, sai naji na dawo daidai kamar ba Ni ba, sai ciwon kan kaɗan -kaɗan shima. Ta dube ni tace, "Me ya haɗa ki da ƙawar taki har rai ya ɓaci ki ka fita hayyacinki ki kai mata wannan uban duka Jiddah? Kin ga yadda kika sauya mata kamanni kuwa? Ba yadda ba ai ba a kama ki amma da kin fasa ƙara sai ki zubar da mutanen da suka riƙe ki, tana can sai dai aka ɗauke ta a mota aka nufi gidansu da ita, don nasan duk kwanakin nan ba zata iya hassala ma kanta komai ba, idan ma Allah Ya taimaka baki ji mata ciwon cikin jiki ba, a na wajen kawai ya tsaya."
Nace ina dubanta, "Ni dai ban da ta cewa domin dai nasan na ji tana ta min magana kan na yi faɗa da Deeni kaina ya fara sarawa na dinga jin amon muryarta na amsa amo a cikin kaina kamar zata fasamin kunne,daga nan ban san abin da ya sake faruwa ba, sai ganin mutane nayi kewaye da Ni... Sallamar Binta tasa nayi shiru domin daman na kai ƙarshen maganata Ni.
 
"Sannu Jiddah, Yau dai wallahi na ji daɗi, ke ana zagin aljanu amma Ni Yau na shiwa naki albarka. Na rantse da Allah tun ranar da kika iske ta naso ki haɗa su duka ki maganinsu amma sai kika tsaya kukan zuci, wanda hakan yasa ta samu damar dawowa har tana maki magana don bata da kunya, ai yanzu sai ta yi hankali idan zata yi idan baya yi kuma ta sake dawowa na rantse da Allah babu mai cetonta duk nan unguwar."
 
Mamarsu Khairat ta dubi Binta, "To wai me ya haɗa su ne?" Kamar daman jira take, ta kwashe komai ta gaya mata. Ta kwashe da dariya tace, "Amma fa ba ƙarya ta jibgu,mu fa ihu muka dinga ji muka rasa daga ina ne, saboda ba wanda ya kawo gidan Jiddah ne, to ita da miji ma yana can yana girbar abin da ya shuka wa zai tsammanin faruwar wani abu a gidanta? Sai da mu ka ji abin ya yi yawa sannan fa muka nufo nan gidan, Safiya ta yi laushi har ta kasa ihun sai numfashi take idanunta sun firfito tul kamar an jefa fulawa a man zafi (fanke) wallahi da ƙyar muka samu aka ƙwace ta, daga hannun Jiddah. Ashe Jiddah nada aljanu? Wallahi bamu taɓa sani ba, ko da naji ashe shi yasa tai ma Deeni munafikin duka har ya tsage ƙashi?" 
Ni dai sai kuka ya ƙwace min wane irin aljanu kuma gare Ni? Yaushe na same su? Ina na haɗu da su? Me yasa jarabtar rayuwata ƙara yawa take madadin raguwa? 
 
To mu bi Haupha don jin dalilin hakan.
Shin yaushe Deeni zai dawo gidansa?
Wane mataki zai ɗauka idan ya ji an gabji Safiya?
 
Taku a kullum Haupha!!