WATA UNGUWA: Fita Ta 23
BABI NA ASHIRIN DA UKU
Sorfina ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ta ce "Shi kenan sister tun da wannan ita ce rayuwar da kika zaɓawa kanki ban isa na hana ki ba, ko da ma ni ban taimake ki ba na san zaki fita farautar cikar burinki ne, a lokacin ban san wane hali zaki faɗa ba. Har gara ki zauna da ni."
Mahee ta gyara zama ta ce "Na gode, ina so ki sani ina da dalilina na fantsamowa duniya da neman shiga wannan harkar ido rufe."
"Kada ki damu bariki gida kika zo, domin ni ma nan da kike ganina duk kanwar ja ce, cikakkiyar 'yar bariki ce lamba ɗaya. Ko a jiyan da muka haɗu na dawo ne daga ziyarar wani gayena."
Da mamaki Mahee ta ce "Taya kike yawon bariki da aurenki?"
Yar dariya Sorfina ta yi sannan ta ce "Fu'ad ba mijina ba ne kamar yadda kika yi tsammani shi ma zaman dadiro muke yi, wannan gidan da kika gani shi ya mallaka mini shi da kuma motoci guda biyu da nake hawa."
Maheerah ta saki baki tamkar gaula, "amma yar'uwa ke me ya sanya kika fara wannan harkar?"
Jin haka ya sa Sorfina ta dafa ta tare da faɗar
"Labari ne mai tsayi idan lokaci ya bada dama a gaba zaki ji, sai dai ki sani ni ƙaddara ce ta jefo ni a wannan harkar daga bisani daɗin ƙaddarar ya ratsa ni har bana so wannan ƙaddarar ta kauce mini."
Maheerah bata ce mata komai ba, sai ita ce ta sake cewa "Yanzu ki tashi ki yi break, ki kwanta ki ƙara hutawa gobe idan kin samu sauƙi sai mu je mall da boutique domin ki zaɓi kalar suturun da kike son yin amfani da su. Shi kuwa wancan uniform naki sai ki bayad da shi wa masu buƙata."
"A'a yar uwa ina da bukatar uniform da jakata ta makaranta a kusa da ni, domin zasu kasance masu ankarar da ni ga abin da na fito nema duk lokacin da wani abu ya so ta shagaltar da ni."
Murmusawa ta yi ta ce "to ai shi kenan."
Maheerah ta ƙarasa kan dinning ta zuba lafiyayyen abinci tana ci, tana yi tana murmushi ita kaɗai. Ko da yake tun da take a rayuwa bata taɓa yin lafiyayyen kari irin wannan ba, ita kanta ta san a yau ta fara more duniya.
Bayan ta ci ta ƙoshi ta koma ɗakinta ta kwanta don ta yi jinyar jikinta.
Washegari Maheerah ta tashi garau sai wasu yan tabo da ba za'a rasa ba a fuskarta, don haka bayan sun kammala haɗa break fast sun ci sai suka shiga gyaran gidan. Da suka kammala ne kowaccensu ta koma ɗakinta ta sheƙa wanka.
Bayan fitowar Sorfina daga wanka ta je ɗakin Maheerah ta janyo ta zuwa nata ɗakin ta bata haɗaɗɗun mayukan shafa da turaruka ta shafa tare da feshe jikinta da turarukan masu sanyin ƙamshi. Sannan ta shiga tsantsara mata kwalliya da kayan shafarta, ba ta wani cika mata fuska ba, ta yi mata kwalliya ne dai dai ita. Bayan ta gama mata kwalliyar ta buɗe walldrop ɗin kayanta ta zaɓowa Mahee wasu fitinannun English wears riga da wando kalar fari da baƙi ta miƙa mata tana murmushi tare da cewa
"Sister gwada wannan mu ga ko zai miki?"
Ta karɓa ta shige toilet ɗin ɗakin ta sako kayan. Ƙarar buɗe ƙofar banɗakin ya janyo hankalin Sorfina ta tattare hankalinta kacokan kan ƙofar.
Maheerah ta fito tana takawa a hankali fuskarta ɗauke da murmushi.
"Wow! Sister kin ganki kuwa? Kayan nan sun masifar amsarki, ke kyakkyawa ce sosai."
Ita ma ta maido mata murmushin sannan ta ce "Na gode Sis."
Ɗan ƙaramin mayafi ta bata ta yane kanta da shi ya tsaya iya kafaɗa. Dama can Sorfina ta riga ta shirya har ta buɗi baki zata ce wani abu sai wayarta da ke ajiye kan madubi ta hau ruri. Cikin hanzari ta ɗauko ta ta ɗaga tana faɗar "Eh dear we are ready, gamu nan."
Tana kashe wayar ta ja hannun Maheerah bayan ta ɗauki jakarta ta kulle ɗakunan sannan suka fita.
A compound suka tarar da haɗaɗɗiyar motarshi har ya faka ta tare da buɗe kofofinta, suna zuwa kawai shiga suka yi, ya murza stiari sai ARG MALL shi ne babban mall na garin.
Shigarsu ke da wuya wani sauti ya ratsa kunnuwansu ana faɗar "London girl kina fire fa." Sorfina ta ɗaga wa gayen hannu ba tare da ta yi magana ba. Kasancewar Fu'ad yana wajen mall ɗin a mota yana jiransu saboda yau faɗin rai yake ji.
Suna cikin zagayawa ne idon wani Alhaji mai ji da dala ya sauka kan Maheerah saboda haka ya matso daf da ita har tana iya jiyo numfashinsa ya ce "Hi Baby! Kin min kyau, ya ko zamu jone?"
Juyawar da Sorfina zata yi don ganin ko waye idonta ya sauka kan shi sai ta ja da baya tana zazzare ido tare da faɗar "Inah! Impossible, ba zan taɓa bari hakan ta faru ba...."
Ummu inteesar ce
managarciya