HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 26 

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 26 
HAƊIN ALLAH
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
 
 
           Page 26
 
 
 *Ku yi haƙuri kwana biyu kun ji Ni shiru, ku sakani a dukkan addu'arku don Allah.* 
 
Washegari tunda safe suka nufi gidan yarin cike da abubuwa da dama a ranau. Barista Alawiyya na tunanin su waye suke da alaƙa da mahaifiyarta akan wannan kisan? Me yasa mahaifiyarta ta makance ne? Tana da tarin tambayoyi da take da buƙatar ace mahaifiyarta ta amsa mata su, sai dai matsalar guda ce ga alama mahaifiyarta ta riga ta gaji da duniyar duba ga yadda abubuwa suka faru da ita na rayuwa, tabbas ba zata taɓa barin hukuncin kisa ya tabbata ga mahaifiyarta ba, ko da hakan na nufin abubuwa da dama ne zasu faru kuwa. Ya zama tilas ya zama lallai ta bibiyi masu bibiyar mahaifiyarta, dole ne ta nunawa duniya wannan karon shari'ar tata ce, da ita ake karawa ba karewa take ba, ya zama wajibi tai shari'ar da za ta finciko duk wani alhaki da ke mallakin mahaifiyarta ta miƙa mata. Tsurama motar Daddynta ido tai, "Sai dai kai haƙuri Daddy amma wannan karon hatta ahalinka sai na ɗanɗana masu abin da suka ɗanɗana mata na raba ta da mijinta suka barta da ƙaramar yarinya ba ci ba sha na tsawon shekaru wanda hakan sun karya doka ta shafi na dubu ɗaya da dari bakwai da tamanin da uku ne (1783). 
 
Dr Falsal ya kalleta, "Don Allah ki natsu ki kwantar da hankalinki, domin nasan cewa tunda Allah Yasa kika amshi wannan case to ya zama tarihi ba abin da zai shafi Mama da yardar Allah zata fice daga wannan yanayin. Kinga tunda muka taho baki yi maganar yara ba, bayan kin san suna makaranta muka taho muka barsu, har mun kwana... Wani banzan kallo ta maka mai wanda yasa ya rufe bakinsa ba tare da ya shirya ba. Tabbas Alawiyya nada haƙuri da kauda kai, amma fa idan ranta ya ɓaci tamkar bata san yadda kalmar mutunci take ba ko haƙuri, lokacin da mutane ke gaya mai yana auren mace-namiji dariya suke ba shi, wai har tambayarsa ake anya bata dukansa? Saboda yadda take da zafi kan aikinta uwa uba ta sha kamo ƙattin maza da kanta ta kai su gaban Shari'a musamman idan ta danganci fyade ko mijin dake wahal da matarsa. Duk jinsu yake domin shi ko cacar baki bata yi da shi, duk da yana mata faɗa musamman kan yaransu amma sai dai ta ba shi haƙuri tai tsit bata sake magana. Sau ɗaya ne watarana suna tafiya a mota za su wuce daidai gadar Gaida road suka ga wani magidanci ya dage sai dukan matarsa yake ga ciki ga yara uku sai kuka suke suna riƙe shi, amma har su kaima duka yake yana ƙara komawa kan mahaifiyar tasu. Duk ga mutane amma sai suka tsaya kallo wasu ma har ɗauka suke a waya ba ruwansu da zuwa su raba faɗan. Shima dai kamar kowa ne mai mota fakin ya yi kawai yana kallon yadda mijin ke dukan matar tana ta kare cikinta tana kuka. Kawai ganin Alawiyya ya yi gun bai san lokacin da ta buɗe motar ta fice ba, sai hango ta ya yi ta ɗauke mijin da mari hannu bibbiyu, kamar a Film ya ga ta dage iyar ƙarfinta tana jibgar mutumin nan, ganin tana niyyar lahanta shi yasa ya fice da sauri ya nufi gun da zummar janye ta, lokacin ta dunƙule hannu zata sauke shi kan cikin mutumin ta sauke mai shi a kumatu, sai da haƙorinsa ya fice don azaba. Ganin mijinta ta daka yasa ta sake fusata amma sai ya yi ta maza ya sake karewa dole ta haƙura ta  nufi mota nan take tai waya, ba a jima ba sai ga ƴan sanda sun iso gun da motar asibiti, ta dube shi ba wasa ta ce ya je asibiti a duba shi ita kuma zata je office tare da matar da yaran yanzu, su yi waya idan an gama mai za ta je ta ɗauko shi. Ta dubi mutanen dake gun ta daka masu tsawa tana cewa, "Wai ku nan mutane ne ko dabbobi masu ƙafa biyu hannu biyu? Ko da yake nasan ko dabbobi idan suka ga ƴan'uwansu dabbobi na cutar junansu shigar masu su ke amma ku sai abin ya zame maku abin nema da tutiya, to wallahi duk wanda ya sake ya ɗora wannan abin sai na kama shi na ɗaure nasa an ci shi tarar manyan kuɗaɗe. Kar ku manta sunana Barista Alawiyya Bello Gareji."  Nan da nan mutanen kowa ya watse yana gogewa kar da ya jawa kansa bala'i da rana tsaka dan kowa yasan wacece Barista Alawiyya Bello Gareji a Kano da kewayen Kano da sauran Jahohi don babu inda ba a ɗaukar ta aiki kuma indai ta je sai ta ci nasara.
Cikin matuƙar tausayawa ta kama matar ta shiga motarta, suma yaran suka shiga kai tsaye babban asibitin ta dake unguwar Bachirawa ta nufa da ita don a duba lafiyarta data abin da ke cikinta. A takaice sai data sa mijin yin gidan yari ta kuma tsaya tsayin daka kotu ta raba auren ta kuma mallaka ma matar gidansa, kyauta har da tarar wasu iyayen kuɗi da zai ba da don kula da yaransa da cikin dake jikinta, wanda sai dai danginsa su kai karo-karo suka haɗa kuɗaɗen tilas aka ba matar. Haka bai manta ba da shari'ar da ta gwabza da ɗan gidan ministan harkokin waje na garin Abuja wanda yawon shan iska ke kawo shi Kano ya yi wa ɗiyar wata almajira fyade har ta mutu, cikin jarida ta tsinci labarin amma sai da t upai ruwa tai tsaki matsayinta Na babbar Lauyar dake zaman kanta ta shiga case ɗin ta dinga gogawa da lauyan ƙasar waje da Uban yaron ya ɗauko kan a kare mai yaro, amma ƙarshe sai da ta kai Yaron gidan yari, kuma ta sa Uban ya biyya diyya tunda yana tarin dukiyar da yake ba yaran na abin da ya ga dama. Ganin hakan Uban ya dinga turo mata ƴan daba kala-kala amma sai dai ta tura mai su asibiti kawai ya rasa yadda akai ma take masu wannan laga-laga. Don kuwa shigowar ƴan fashi gidansu har bai iya ƙirga yawansu, sai dai ya ga ta ci riga da wando kamar wata ƴar China ta kama artabu da su sai ta kama su. Shi ya rasa inda ta koyo wannan shegen faɗan ma wallahi. Shafa inda ta cire mai haƙori ya yi ya sauke ajiyar zuciya ya sadda kansa tabbas yana da buƙatar ya kama bakinsa idan ba haka ba kuma yana da kyau ya tattara ya koma gida gun yaransa ya jira ta, idan ta gama ta dawo gunsu. Daram! Gabansa ya faɗi ya ji jiya tana cewa idan an isa a fara kama shi da Daddy sannan a kira ta a waya! Tabbas Alawiyya tafi aljani iya shaiɗana gata bata da tsoro ko da wasa, yanzu ta ya zai iya nufar Kano bayan neman a ɗauke shi ake?"  Jin alamar an tsaya da motar yasa ya dawo hankalinsa ba tare daya ba kanshi amsar tambayar da ya yi ba.
 
Tare suka shiga ciki, fuskar Alawiyya sam ba annuri hatta Daddyn ya lura da yadda ta tsare gida take ɗauke kai. 
 
Bayan sun nemi a fito masu da Fatimar suka zauna kan babban kafet ɗin da Dr Falsal ya shimfiɗa masu kowa da abin dake damunsa.
 
Daddyn Alawiyya na cike da tsoron kar dai ace da gaske ya sake rasa Fatima duk tsawon shekarun daya ɗauka yana jiranta. Hawaye suka zubo min bai damu daya goge ba.
 
Barista Alawiyya na tunanin yanzu a nan mahaifiyarta ta kwana, cikin fitsari da kashi da cinnaku da sauran abubuwan ƙyama?" Hawaye suka zuba mata bata damu data goge ba ita ma.
 
Dr Falsal na tunanin yanzu kenan rayuwarsa na cikin tashin hankali saboda matarsa? Kenan wannan karon zata iya bijire mai idan yace ga wani abun kan mahaifiyarta? Tabbas akwai damuwa mai tarin gaske, a Yau ji yake yana jin wani abu mai kama da nadama tare da danasanin barin Alawiyya ta zama yadda ta zama na amsa sunan babbar Lauya.
 
Shigowar Fatima gun yasa kowa tashi tsaye yana kallonta, Alawiyya ta tashi da sauri ta tarbo ta cikin sauri ta kai ta gun da zata zauna.
 
Cikin lalube ta zauna tana riƙe da hannun Alawiyya, ta zauna bakinta ɗauke da "Allah Ya yi maki albarka." 
 
 
Bayan kowa ya zauna, Barista Alawiyya ta gaida Fatima ta amsa shima Faisal ya gaida ta, ita kuma ta gaida Daddyn Alawiyya.
 
Barista Alawiyya ta dubeta cike da tausayi ta ce, "Mama na gani a labarai an ce ku uku ne gun maidiganku amma ban ga maganar su a cikin case ɗin kisan kan ba, sannan kuma na gani an ce kin yanka shi ne sannan ki ka caka mai wuƙa a ciki...
 
 "E tabbas haka ne duk na aikata! 
 
Hawaye suka zubo ma Daddy, yayin da Alawiyya tai murmushin yaƙe ta dubi Mamarta tace, "Naga an saka cewa ke ce amarya kuma ke ce kawai kika taɓa haihuwa da shi a gidan don haka kika kashe shi don ki samu gado...
 
"E haka ne nice na kashe shi!
 
Kallonta kowa yake ban da Alawiyya data sadda kanta ƙasa hawaye na son zubo mata amma ta ƙi basu damar zubowa.
 
"Tabbas Mama ba ke ce ki kai kisan kan nan ba." Cewar Alawiyya.
 
"Na rantse da Allah nice na kashe Alhaji Alawiyya! Don Allah kar da ki saka kanki a halaka domin Ni daman can rayu cikin farin ciki ba, don haka kada ki hanani komawa gun mahaliccina domin ina kyautata zaton insha Allah zan kasance a cikin farin ciki a can. Alawiyya bari ki ji dama ina cike da nadamar tafiyata ban ganki ba, banga mahaifinki ba naga wane irin yanayi kuke to alhamdulillah tunda ga dukkan alama baki da damuwa har shi sai ince Allah Ya ƙaddara saduwarmu a can don nafi son mutuwa da rayuwata."
 
Barista Alawiyya "Kenan kina nufin don ki mutu kema kika kashe mijinki?"
 
Fatima, "Nice dai na kashe shi!
 
Barista Alawiyya, "Ba ke kika kashe shi ba, tun yaushe kika makance?"
 
Fatima, "Shekara tara data wuce."
 
Barista Alawiyya, "Makaho na iya yanka Kaza ne?"
 
Fatima, "Nice na kashe Alhaji da hannuna."
 
 
Barista Alawiyya ta dubi mahaifiyarta cike da tarin damuwa tace, " Mama bayan rabuwarmu dake wace irin rayuwa kika kasance ne ?"
 
 
Wani irin kuka mai karfi ya ƙwace mata, wanda kowa sai da ya kalleta .
 
Barista Alawiyya tayi murmushi ta zo gun da take buƙata, don haka ta dubeta tace, "Alokacin da za ki bi mijinki babu irin roƙon da ban yi maki ba amma kika tsallake ni gaban Inna kika bi mijinki baki ko jin tausayina matsayina na wadda na rasa Uba kuma Uban nawa ke ce ya ba amanata saboda yasan ke ce kawai za ki iya jure zama da Ni duk rintsi duk wahala, amma saboda son mijinki ya rufe maki ido kika watsar da ni kika bi shi batare da ko waigena kin yi ba...
 
Fatima ta fashe da kuka sosai tace, "Don Allah Alawiyya kar da kice min duk tsawon lokacin nan kina riƙe da Ni a zuciyarki ne? Tabbas Alawiyya nayi godiya ga Allah tafi dubu lokacin da na bi mijina ban tafi dake ba, saboda da yanzu kin jima da barin numfashi Alawiyya."
 
Sai tai shiru kamar wadda aka rufe wa baki.
 
Barista Alawiyya ta dube ta tace, "Lokacin da kika tafi ita ma Inna tafiya tai har Yau bata dawo ba."
 
Fatima ta zabura tace, "Wallahi Alawiyya dole ce tasa na ƙyale ki ban sake nemanki ba, domin nima rayuwa nayi tamkar matacciya kawai banbancina da matacciya shi ne ina numfashi haka ana bautar da Ni ana amfani dani gun abubuwa masu yawa wanda ko da yaushe ji nake ina ma ace mutuwa nayi madadin rayuwar da nake mai cike da son kai da son abin duniya? Tabbas Alawiyya rayuwata bata da wani amfani ta baya da na bayyana maki ita, ko da yake akwai wani sirri wanda zai min katanga gun bayyana maki bayan rabuwarmu wanda nasan sai bayan an yanke min hukunci gobe kamar yadda aka gayamin zai bayyana saboda ita gaskiya bata taɓa ɓoyuwa sai dai ta jima bata bayyana ba."
 
 
Barista Alawiyya, "Kina nufin gobe ne za a fara zaman kotun?"
 
Fatima, "E haka aka gayamin ɗazun za a shiga dani kotu gobe gun da ban da kowa ba mai kareni. To nima murna nake da kashe Ni da za ai domin na gaji da rayuwata Ni kaɗai babu ahalina ban da kowa Alawiyya sai fa ke to zuwana a rayuwarki yana nufin kema zan shafa maki kashin Kaji ne don haka zan tafi kotu gobe da ƙwarin gwiwar amsa duk wata tambaya kamar yadda aka gayamin amsar da zan bada saboda ina sonki rayu Alawiyya ban san a ce baki ɗaya zuri'armu ta shafe a doron duniya."
 
 
Cikin kuka Alawiyya tace, "Tabbas ahalinki ba zai taɓa shafewa ba a doron duniyar nan ba Mama domin yanzu haka kina da jikoki guda uku mace guda namiji ɗaya yanzu haka ina ɗauke da wani cikin wanda nake saka ran wasu ƴan biyunne ko ƴan uku a cikinsa, kin ga kau ai zamu yaɗu a duniyar muma ba zamu gushe ba."
 
Fatima ta rungume Alawiyya tana kukan farin ciki mai cike da jin daɗi, ita ma ashe ta zama Kaka,tana da jikoki har guda uku.
 
Barista Alawiyya ta ci-gaba da cewa, "Ina son ki sani cewa kina da ɗiyar da zata iya jan tunga a gaban kowa ta ƙwatar maki ƴancinki ta goga da kowa a kanki ta shiga ta fita ta tabbatar da cewa kin amshi haƙƙinki gun waɗanda suka ƙwace maki shi, saboda Ni ɗin Barista ce aikina kenan ƙwatar ma wanda aka cuta haƙƙinsa. Kin ga kuwa ɗan Malam ya yi rawa an masa liƙo ina ga ɗan makaɗi? Kawai ki gayamin gaskiyar abin da ya faru karki damu da komai kina tare da gatanki kamar yadda kowa ke tare da ni gatan Mamana."
 
 
Fatima ta zabura hankali tashe tace, "Dama kece Lauyar da ake ta maganar ta tsaya min,za a kashe ta?" To idan dai na isa dake kin amince cewar nice na haifi ke to ina son ki janye daga wannan shari'ar saboda ban san na rasaki ban san ki shiga damuwa bayan wadda kika shiga a baya."
 
Kawai ta tashi tana neman hanyar tafiya ranta a ɓace.
 
Daidai nan wayar Dr. Faisal tai ƙara, wayar Daddy tai ƙara ita ma Barista Alawiyya wayarta tai ƙara.
 
Baki ɗaya suka ɗaga kiran suna sauraren abin da ake gaya masu lokaci guda.
 
Tare suka aje wayar kamar an basu umarni a tare suka kalli juna,ba wanda yace ƙala.
 
Ko me aka gaya masu? Anya kuwa Fatima zata ba Barista Alawiyya Bello Gareji damar yin aikinta yadda ya kamata?
 
Shin wane mataki Barista Alawiyya Bello Gareji zata ɗauka a wannan shari'ar?
 
 
Don Allah ku yi min afuwa abubuwa ne suka cakude min kwanakin nan don haka kuke jina shiru.
 
Taku a kullum Haupha!!!!