Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da babura 1000 da Keke Napep 500 don taimakawa sufuri

Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da babura 1000 da Keke Napep 500 don taimakawa sufuri

Gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da babura 1,000 da masu kafa uku 500 da za ta sayar wa al’ummar jihar kan farashi mai rahusa.

Wannan wani bangare ne na dabarun da gwamnan jihar, karkashin jagorancin Ahmed Aliyu ya bullo da shi. domin inganta rayuwar matasan jihar.

A cewar sanarwar da mai magana da yawunsa, Abubakar Bawa, ya kuma rabawa manema labarai a ranar Juma’a, a karkashin shirin, za a siyar da babura da babura masu kafa uku ga masu son saye bayan an ajiye wasu makudan kudade.

Ta wannan hanya, daga baya, mai shi zai ajiye wasu adadin kudi duk wata har sai ya biya kudin babur ko babur da ya karba.