Gwamnan Matawalle ya tabbatar da dokar kisa ga masu ba da rahotan siri ga 'Yan Bindiga 

Gwamnan Matawalle ya tabbatar da dokar kisa ga masu ba da rahotan siri ga 'Yan Bindiga 

Daga Hussaini Ibrahim 

 

Gwamnan jihar Zamfara Hon Bello Matawallen Maradun ya sanya hannu da tabbatar da  dokar da 'Yan majalisar Dokokin jihar tayi na Kisa ga wanda aka kama da hannu cikin 'Yan Bindiga  Masu Garkuwa da mutane da masu ba 'yan Bindiga rahotan siri a Zamfara. 

 
Matawallen Maradun ya sanya ma dokar hannu ne ayau bayan Shugaban Majalisar dokokin jihar Muazu Magarya ya gabatar masa da Dokar a gidan gwamnatin da ke Gusau. 
 
A cikin dokar akwai daurin rai da rai ga masu satar shanu. Kuma za'a kafa akwati na amsar koke daga jama'a a gaban gidan gwamnatin dan  zamu nasara kawo karshen 'Yan Bindiga da masu Garkuwa da mutane. 
 
Gwamna Matawallen yayi kira ga jama'a da suji tsoran Allah wajan bada bayani siri a cikin wannan akwati. 
 
Shugaban Majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon Muazu Magarya ya bayyana cewa, sunyi wadannan dokokin ne dan samarwa al'ummar jiharZamfara mafita me dorewa.