Hare-Haren da Ake Cewa Boko Haram Na Kaiwa a Najeriya Karya Ne---Buhari 

Hare-Haren da Ake Cewa Boko Haram Na Kaiwa a Najeriya Karya Ne---Buhari 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, a yanzu babu wani bangare a Najeriya da ke karkashin ikon ‘yan ta’addan Boko Haram. 

PM News ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban zauren zaman lafiya na Abu Dhabi, Shaykh Abdullah Bin Bayyah a ranar Talata 17 ga watan Janairu. 
Sun yi wannan ganawa ce a wani taron zaman lafiya da aka gudanar Nouakchott ta kasar Mauritania, inda Buhari ya ce gwamnatinsa ta kwace ikon Boko Haram a kasar. 
Da yake bayanin cewa, labaran hara-haren Boko Haram a Najeriya duk na karya ne, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa, masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar suna da nufin raba ta ne. 
“Boko Haram karya ce. Kun ce ilimin zamani na yammacin duniya haramun ne. Yaudara ce. 
Duk wanda ke daukar nauyinsu so yake ya raba kasar. “Dukkan wuraren da suka kwace kafin mu zo mun kwato su, kuma muna ci gaba da sake gina yankunan.”