Jirgin ruwa ya nutse da mutum 20 da suka tashi daga kauyen Dundeji zuwa Kambama a karama.r huƙkumar Shagari ta jihar Sakkwato.
Mutanen sun bar gidajen a ranar Talata da misalin 12 na rana domin tafiya samo itacen dafuwa sai jirgin ya nutse da su gaba daya.
Masu aikin ceto sun tsamo mutum 15 a mace ana neman biyar a yanzu haka ba a gansu ba.
Gulbin kusan duk shekara sai mutane sun nutse a cikinsa tare da samun salwantar rayuwa.
Sauran bayani na tafe..





