Na Cika Alkawalin Da Na Daukarwa Katsinawa---Gwamna Dikko

Na Cika Alkawalin Da Na Daukarwa Katsinawa---Gwamna Dikko
 

Gwamna Dikko Umar Radda na Katsina ya ce ya cika alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓensa. 

Gwamnan ya ce a cikin watanni takwas da ya kwashe kan kujerar mulki, ya cika alƙawuran da ya yi wa al'ummar Katsina, cewar rahoton jaridar The Nation.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa wacce ke ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labaran jihar Katsina, Bala Salisu Zango. 
Dikko ya kuma yi alƙawarin ci gaba da samar da abubuwan more rayuwa a jihar Katsina.
Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin alƙawuran da ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe waɗanda ya cika sun haɗa da tsaro, ilimi, samar da ruwan sha, kiwon lafiya, sake fasalin hukumomi da dai sauransu. 
Wani ɓangare na sanarwar na cewa: "Gwamnatina ta ɗauki malamai 7,325, ta ba ƴan asalin jihar Katsina guraben karatu a ƙasashen waje don yin karatun likitanci a Masar, ta sayo takin zamani domin noman damina."
"Gwamnati ta rabawa marasa galihu tallafi, sayan magunguna da kayan aikin asibiti, gyara cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar da ɗaga darajar ƙananan asibitoci biyu matakin babban asibiti da dai sauransu."