Korbit Table Water na gabatar muku da sabbin Dispenser mai Famfunan Lantarki  Atomatik

Korbit Table Water na gabatar muku da sabbin Dispenser mai Famfunan Lantarki  Atomatik

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

A ƙoƙarin samar da ruwan sha mai tsafta, lafiyayye da araha, Korbit Table Water, babban kamfanin samar da ruwa, ya ƙaddamar da sabon samfurin Korbit Dispenser, iri na farko a kasar nan, mai dauke da Famfon zamani. 

 Shugaban kamfanin, Alhaji Garba Ahmed Ibrahim ne ya sanar da hakan a tattaunawarsa da Alfijir Labarai, inda ya bayyana inganci da kuma samun saukin wannan sabon samfurin. 

Ya kara da bayyana cewar Kwalbar Dispenser din Korbit yana da famfon ruwa na lantarki mai caji ta atomatik, sabanin wanda ake da su a baya. 

Tare da wannan samfurin, abokan cinikin mu za su iya jin daɗin fa'idodin ruwan sha mai tsafta cikin yanayi mai sauki. 

Kamfanin ya saukaka wa abokan cinikinsa samun kwalaben Korbit ta hanyar samar da shi a rumfunan Dillalanmu manya da kantunan da ke fadin kasar nan, wadanda suka hada da Sahad Store, Best Medix, Sadaraki, DanAljanna, Jujin Labbu, da sauransu. 

Alhaji Garba ya kara da cewa ga masu sha awar cinikayya da mu, tsofaffi da kuma sabbin customers, suna iya ziyartar waɗannan wurare da aka lissafa a sama ko tuntuɓar kamfanin kai tsaye ta lambobin wayar:

08123172526, 08166665444, ko 08096233122. 

Korbit yana alfahari da sadaukar da kai ga inganci da aminci.

Hakazalika kamfanin yana amfani da sabuwar fasahar zamani don tabbatar da cewa ruwansu yana fuskantar tsauraran matakai na ingantawa tayin amfani da Reverse Osmosis (R.O.) da Ozone Generator wa'yanda suke kalkale ruwan sha.

Ɗaya daga cikin mahimman fa'idodin zabar ruwan tebur na Korbit shi ne kokarinsa na kiyaye ɗanɗano tayin amfani da kyakkyawan mazubi domin samar da tsaftataccen ruwan sha ga kowa da kowa.