Lamido Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Sarkin Gabas Na Ambarura

Lamido Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Sarkin Gabas Na Ambarura

 

Dan takarar Sanata a gabascin Sakkwato cikin jam'iyar APC Alhaji Ibrahim Lamido ya yi ta'aziyar rasuwar Sarkin Gabas na Ambarura Alhaji Muhammad Tukur wanda ya rasu a yau Laraba bayan fama da jinya. 

Lamido a wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar wadda ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai ya bayyana rashin basaraken a matsayin babban rashi ga mutanen Ambarura da karamar hukukamar Illela da jihar Sakkwato baki daya.
Ibrahim Lamido ya bayyana Sarkin Gabas na Ambarura na farko da ya bar duniya da shekara 78 mutum ne hakuri da sanin yakamata  ya bar gibi wanda zai yi wahalar cikewa.
Lamido ya mika ta'aziyar margayin ga iyalansa da ya bari waton matan aure biyu da 'ya'ya 12, mace shida da maza shida, Allah ya gafarta masa ya sa ya huta, su kuma ya ba su hankurin rashinsa.