Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Naɗin Sarautu  Da Aminu Tambuwal Ya Yi

Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Naɗin Sarautu  Da Aminu Tambuwal Ya Yi

 

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu, ya kafa kwamitin mutane 9 da za su  duba duk wasu naɗe-naɗe da tsohon gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya yi a gab da ƙarshen gwamnatinsa. Kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan harkokin ‘yan sandan Nijeriya, Muhammad Maigari  Dingyadi, an ba shi aikin duba naɗin wasu sarautu na gargajiya da kuma sauya sunayen manyan makarantu da Tambuwal ya yi. 

Hakan na ƙunshe ne a sanarwar da Malam Abubakar Bawa, sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Sokoto ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 
Sanarwar wacce aka fitar a ranar Litinin, ta kuma ce kwamitin zai duba batun sauyawa makarantu wuri, da naɗin shugabanninsu da gwamnatin da ta shuɗe ta yi. 
“Za kuma su sake duba duk wasu naɗe-naɗe na gargajiya da tsohon gwamna Aminu Tambuwal ya yi a baya-bayan nan tare da magance korafe-korafen da aka yi kan wasu daga cikin waɗanda aka naɗa.” 
A lokacin da Aliyu ya hau karagar mulki ya soke naɗin sarautun gargajiya da abin ya shafa tare da bayar da umarnin soke sauya sunayen manyan makarantun. 
Rahoton The Guardian ya ce gwamnan ya kuma rushe shugabannin manyan ma'aikatu da sauran hukumomin jihar. Mambobin kwamitin da aka sun haɗa da Bature Shinkafi, Dakta Kulu Abubakar, Isa Sadiq-Achida, Suleiman S/Fulani, da Dakta Umar Yabo a matsayin Sakatare, da dai sauransu.