Doka ta bada damar soke sabbin ma'aikatan da Ganduje ke ɗauka a jihar Kano--Barista A.U. Hajji

Doka ta bada damar soke sabbin ma'aikatan da Ganduje ke ɗauka a jihar Kano--Barista A.U. Hajji

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Tun bayan zaɓen aka gudanar na 20 ga watan Maris 2023, da aka ayyana Engr. Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen. rahotanni sun nuna cewa, gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta dauki sabbin ma'aikata a ɓangarori daban-daban, 

Barrister Aliyu Usman Hajji babban lauya ne mai zaman kansa a Nigeriya, ya bayyana cewa  duk da ya ke doka ta baiwa Dr. Abdullahi Umar Ganduje damar daukar aiki amma Gwamna mai jiran gado Engr. Abba Kabir Yusuf zai iya soke duk wanda aka dauka ba bisa ka'ida ba, 

A tattaunawar da ya yi da Jaridar Blueprint Manhaja, Barrister A.U Hajji ya bayyana cewa "Idan aka duba kudin tsarin mulki Nigeriya a sashi na 5 ya baiwa Gwamna dama da ikon  daukar aiki kaitsaye a jiharsa a dokance, amma  fa hakan ba ya nufin ya yi ta daukar aiki barkatai ba, gwamna Ganduje a kalla ya yi shekaru 8 ya na mulkin Kano amma ba a ga yana ta daukar aikin mai yawa ba, sai yanzu? Don haka dole zai kawo alamar alamar tambaya.

A.U. Hajji wanda yanzu haka dalibin PHD ne akan Shari'a ne a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya cigaba da cewa, "Yanzu da ace dan jam'iyya gwamna Ganduje ne zai karɓi mulki anya zai yi haka? Kuma mai ya sa a 2019 bai yi haka ba sai a yanzu da ya ke bankwana da jihar Kano? Sannan kuma wannan daukar aikin alfanu zai kawowa jihar ko rashin alfanu?

Amma tabbas doka ta bashi dama daukar aiki, duk da yake ba kowane aiki zai iya dauka ba, wani sai ya dangana ga majalisar dokoki jiha,  amma lallai wannan daukar aikin a doron doka akwai alamar tambaya, 

"Kuma ko da a wajen daukar aikin an cika ka'idoji da sharuddan  daukar aiki, to idan Abba Gida-gida ya zo zai iya soke daukar aikin, illa iyaka shi zaɓaɓɓen ya cika ka'idoji da dokoki da ake bi idan an soke daukar aikin mutum shikenan, idan kuma bai cika ba shi ma za a iya kaishi kotu domin ya cika". inji Barrister A.U. Hajji