Yakin Sudan: Gwamnatin Nijeriya Za Ta Fara Kwashe 'Yan Kasar Ta

Yakin Sudan: Gwamnatin Nijeriya Za Ta Fara Kwashe 'Yan Kasar Ta

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a kwashe yan Najeriya da ke makale a yakin kasar Sudan zuwa wani wuri da ke da zaman lafiya a yau Lahadi, 23 ga watan Afrilu da Litinin, 24 ga watan Afrilu. 

Garba Shehu, babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin labarai shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi. 
Ku tuna cewa yan Najeriya na ta matsawa gwamnatin tarayya kan ta gaggauta kwaso yan kasar musamman dalibai daga kasar da ke fama da yaki.
Kasar Sudan ta tsinci kanta a cikin sabon yaki yayin da shugabannin soji biyu ke fada a kan mulkin kasar.
 A yan awanni da suka gabata, rundunar sojin kasar sun ta baiwa kasashen waje damar kwashe jakadu da yan kasarsu, kuma tuni wasu kasashen suka fara yin hakan, ciki harda kasar Amurka. 
Da yake martani a kan ci gaban, Shehu ya ce gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don tabbatar da ganin cewa an kwashe dalibai da sauran yan Najeriya da ke cikin tashin hankali a kasar zuwa wani waje mai zaman lafiya tsakanin yau da gobe.