Gwamnatin Mali ta Ayyana Dokar Ta-Ɓaci A Kan Ambaliyar Ruwa

Gwamnatin Mali ta Ayyana Dokar Ta-Ɓaci A Kan Ambaliyar Ruwa

Daga Abbas Yakubu Yaura.

Gwamnatin Mali ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ambaliyar ruwa bayan mutuwar mutum sama da 30 tare da shafar wasu mutanen 47,000, tun bayan da damuna ta sauka.

Gwamnatin ta yi zama na musammtan domin nazarin matsalar tare da ware dala miliyan bakwai domin samar da agajin abinci da sauran kayayyakin tallafi.

Yawancin shekaru a yankin Afirka ta Yamma da kuma Afirka ta Tsakiya ana fama da ambaliyar ruwa a tsakanin watan Yuni da Satumba.

Ambaliya ta shafi sama da mutum 716,000 a fadin yankin zuwa yanzu a wannan damunar.

A yankin Sahel, ambaliyar ta kashe sama da mutum 200 a Nijar da Chadi, baya ga ɗimbin dukiya da ta lalata.