Gwamnatin Kebbi za ta Magance Kwararowar Hamada a Jihar
GWMNATIN JIHAR KEBBI ZATA MAGANCE KWARAROWAR HAMADA INJI BABBAN SAKATARE.
Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi.
Gwamnatin Jihar Kebbi za ta raba irin itatuwa ga jama’ar Jihar Kebbi kyauta domin shukawa a gidajen su da makaranta da asibitoti da ofisoshi da kuma gonaki da kan hanyoyi domin magance kwararowar hamada a cikin Jihar.
Babban Sakatare a ma’aikatar muhalli da ma’adinai na Jihar Kebbi Alh. Mamuda Umar Kalgo ne ya sanar da haka ga manema labarai a ofishinsa a lokacin da yake zantawa da yan’jarida.
Sakataren yace, idan jama’ar Jihar Kebbi suka amshi irin daga hannun Gwamnatin Jihar Kebbi, kuma su kayi amfani da shi kamar yadda ya dace, to kuwa jihar Kebbi za ta kubuta daga tsunduma cikin ambaliyar hamada ya kara jawo hankali akan wuraren da aka kebe wato gamdun daji da su kula da irin wadannan wurare domin samun nasarar wannan shiri na dashen itatuwa.
Sakataren yace yanzu haka sun tanadi dabino domin dasawa a cikin babban Birnin Jihar Kebbi domin kara kawata babban Birnin Jiha, ya kuma ce itacen giginya da aka dasa tun shekara aru-aru duk sun mutu amma yanzu Gwamnatin Jihar Kebbi ta dauki matakan farfado dasu inda zata rabawa jama’a itacen giginyar domin dasawa a gidaje da gonaki ganin irin alfanun da itacen giginya yake dashi suna da ya‘ya da ake ci itatuwan sa ana rufin daki dasu ya zamanto riba biyu kenan.
Yayi amfani da wannan dama inda yanuna bakin cikin sa ga wadansu shugabannin kananan hukumomi akan yadda suka bari itatuwa da aka rarraba wa kananan hukomomin su a ba’ra duk sun bari itatuwan sun mutu basu kula dasu ba wadansu kuma inda aka aje masu itatuwa ko taba su basu yi ba, amma wadansu shugabannin karamar hukumomin sun yi rawar gani sun rabawa al’ummar su kuma sun sa ankula da su rani da damina.
A karshe sakataren ya jawo hankalin jama’a da su guji saran itatuwa barkatai ba tare da neman izini daga wajen hukumar da abin ya shafa ba, kuma jama’a su sani fa idan babu itace iska zai kada gidaje da makarantu da wadansu gine-gine na gwamnati ko na al’umma.
managarciya