Gwamnatin Adamawa ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70

Gwamnatin Adamawa ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70

Gwamnatin jihar Adamawa ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70 ga ma'aikatanta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ma'aikata sun karbi albashin su na wannan watan a jiya Juma'a, kamar yadda yake a al'ada gwamnatin na biyan albashi a duk ranar 23 ga wata.

Fara biyan mafi karancin albashin, cika alkawari ne da Gwamna Ahmadu Fintiri yayi na fara biyan ma'aikatan daga wannan watan na Agusta.

Wani ma'aikaci mai suna Amos Tumba, ya ce "Karin albashin ya fara aiki kuma an tura min".

Wata ma'aikaciya mai suna Amma Yohanna ta ce " Eh, sun biya, kuma an samu kari".

A ranar 19 ga watan Agusta ne dai, Gwamna Fintiri yayi alkawarin fara biyan mafi karancin albashin a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kwadago.