Na Samu Gwamnatin Wamakko Ba Ta Biya Bafarawa Haƙƙinsa Ba-----Tambuwal

Na Samu Gwamnatin Wamakko Ba Ta Biya Bafarawa Haƙƙinsa Ba-----Tambuwal

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi bayani kan yanda ya biya tsoffin gwamnonin jiha da suka gabace shi hakkinsu abin da ya kai ga ba wani tsohon gwamna dake biyar gwamnati ba shi.

Tambuwal ya furta haka ne a lokacin da ya kai ziyara gidan margayi tsohon gwamna Shehu Kangiwa ya ce "A lokacin da muka shigo mun tarar da gwamnatin da ta shude ta Aliyu Magatakarda Wamakko ba ta biya Bafarawa hakkinsa ba, a lokacin na yi kwamiti a karkashin Ciso Dattijo na ce a je a bincika duk wani tsohon gwamna da ba a biya hakkinsa ba a biya shi, mai girma Shehu Kangiwa a lokacin da ya yi gwamna ana hade ne aka gaya min hakkinsa  ya koma jihar Kebbi, amma na Garkuwa da Aliyu Wamakko aka lisafa aka biya su kuma muka ci gaba da biyansu.

 

"Abin da zance in da akwai wani hakki na Shehu Kangiwa da yakamata wannan gwamnati ta biya shi, na gayyaci Malam Abba ya zo gidan gwamnati zan sa a kafa kwamiti don a sake bincikawa in akwai wani hakki da gwamnatin Sakkwato ta yanzu yakamata ta bayar za mu bayar da shi, in da wata gudunmuwa ma za mu bayar," in ji Tambuwal