An kashe ƴan jarida 68 a shekarar 2024 - UNESCO

An kashe ƴan jarida 68 a shekarar 2024 - UNESCO

An kashe ƴan jarida 68 a shekarar 2024 - UNESCO

Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta ce, karo na biyu a jere, yankunan da ke fama da rikici sun zama wuraren da ke da hadari ga ‘yan jarida da ma’aikatan kafofin watsa labarai, inda a shekarar 2024 aka samu mutuwar akalla mutane 68 yayin gudanar da aikinsu.

Fiye da kashi 60 cikin 100 na wadannan kashe-kashe sun faru ne a kasashe da ke fama da rikici – mafi yawan kaso cikin shekaru sama da goma, kamar yadda sabbin bayanai na UNESCO suka nuna.

“Bayanai na gaskiya suna da matukar muhimmanci a lokutan rikici don taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa da kuma wayar da kan duniya,” in ji Darakta Janar na UNESCO, Audrey Azoulay, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.

“Ba za a yarda cewa ‘yan jarida su biya da rayukansu saboda wannan aiki ba.

“Na kira dukkan gwamnatoci da su kara kokari wajen tabbatar da kariya ga ma’aikatan kafofin watsa labarai, kamar yadda doka ta kasa da kasa ta tanada,” ta kara da cewa.