Karin Wahala A Gaban 'Yan Nijeriya:  Man Fetur Zai Iya Kai N700 a Jihohin Arewa

Karin Wahala A Gaban 'Yan Nijeriya:  Man Fetur Zai Iya Kai N700 a Jihohin Arewa

 

‘Yan kasuwar mai sun yi hasashen cewa litar man fetur zai iya zarce N700 a jihohin Arewacin Najeriya daga watan Yulin nan da za a shiga. 

Wani babban jami’in kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi ya shaidawa Punch cewa farashin fetur zai tashi da zarar ‘yan kasuwa sun fara shigo da mai. 
A watan gobe ne za a fara kawo mai Najeriya daga kasashen ketare. 
A lissafin da Mike Osatuyi yake yi, hakan zai jawo fetur ya kara tsada a Arewa. 
A cewar dan kasuwan, wadanda ke Legas za su rika sayen duk litar fetur a kimanin N600-N610. 
The Cable ta dauko wannan rahoto a ranar Laraba. "Abin da na ke gani shi ne akalla N600, ya danganta da farashin kudin waje, farashin danyen mai a kasuwar Duniya da kuma kudin shigo da man. 
Mutanen da ke Legas za su biya kusan N600, wadanda ke wajen Legas za su biya fiye da N600, wadanda ke Arewa za su rika saye fiye da N700." 
Shugaba hukumar NMDPRA ta kasa, Olufemi Adewole ya shaidawa jaridar cewa a halin yanzu ana cigaba da bada lasisi domin shigo da mai daga waje. 
Da zarar an shiga watan Yuli kuwa, Adewole ya ce kudin da za a saida fetur a gidajen mai ya danganta da yanayin kasuwa a lokacin da kudin kasashen waje. 
Shugaban na NMDPRA ya tabbatar da farashi zai iya tashi, amma ya kara da cewa akwai yiwuwar nan gaba ya sauko idan Naira ta yi daraja a kasuwar canji. 
Baya ga haka, ‘yan kasuwa za su rika karya farashinsu da zarar sun fahimci ba su samun ciniki, masu shigo da fetur za su koma takara da junansu. 
A dalilin daidaita kudin kasashen waje da bankin CBN ya yi, dan kasuwa ya na bukatar sayen Dala kan N765 kafin ya tafi ketare ya shigo da mai.