Gwamnatin Jihar Katsina Ta Bada Tabbacin Yima Masu Ƙaramin Ƙarfi Adalci

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Bada Tabbacin Yima Masu Ƙaramin Ƙarfi Adalci
Gwamnatin jihar Katsina ta sake bada tabbacinta na ganin an yi ma mutane masu ƙaramin ƙarfi adalci a jihar.
Kwamishinan kula da kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki Bello Kagara ya sanar da hakan a lokacin taron ƙarama juna sani na kwana ɗaya wanda ofishin rijistar mutane masu ƙaramin da ake cema SOCU a taƙaice haɗin gwiwa da asusun kula da ƙananan yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF suka shirya kuma ya gudana a ɗakin taro na Katsina Motel.
Taron ya samu halartar masu ba gwamnan jihar Katsina shawara, yan majalisar dokokin jiha, shugabannin ƙananan hukumomin jihar Katsina, wakilan ma'aikatu, ƙungiyoyin farar hula, da dai sauransu.
A lokacin taron ƙarama juna sanin, masu ruwa da tsaki sun yi masayar fahimta da hikimomi akan yadda za a sake shigar da mutane masu ƙaramin ƙarfi cikin kundin rijistar da kuma bunƙasa kundin rijistar don ganin an samu nasarar shirin.
Wasu daga cikin waɗanda aka zanta da su, babban mai taimaka ma gwamnan jihar Katsina akan mutanen da ta'addanci ya shafa da waɗanda aka raba da matsugunansu Sa'idu Danja da shugaban ƙaramar hukumar Danja Rabo Tambaya sun bayyana gamsuwa da kuma shirinsu na tabbatar da ganin shirin ya samu nasara.