Fashewar tankar mai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 77 a Neja 

Fashewar tankar mai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 77 a Neja 

Mutane saba’in da bakwai sun rasa rayukansu a wani fashewar tankar mai Jihar Neja.

Wannan mummunan al’amari, wanda ya faru a yau Asabar, ya jefa al’umma cikin jimami tare da tayar da hankalin jama’a kan matakan tsaro a yankin.

Daraktan Hukumar bada agajin gaggawa  ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba-Arah, ya tabbatar da yawan wadanda su ka rasa rayukansu ga gidan talabijin na Channels a  wata tattaunawa ta waya.

A cewarsa, mutane 25 da suka jikkata an garzaya da su zuwa asibitoci daban-daban a Suleja, Wuse, da sauran cibiyoyin lafiya mafi kusa don samun kulawar gaggawa.