Samar da aiki ga matasa: Gwamnatin Sokoto Za Ta Sayo Babura 1000 da Keke Napep 500 

Samar da aiki ga matasa: Gwamnatin Sokoto Za Ta Sayo Babura 1000 da Keke Napep 500 

Majalisar zartaswar jihar Sokoto ta amince da sayen babura 1,000, tare da keke Napep 500, a wani ɓangare na shirin samarwa matasa aikin yi. 

Hakan na daga cikin ƙudirin da aka cimma a ƙarshen taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a zauren majalisar a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar Tribune.
Majalisar, a taron da gwamnan jihar Ahmed Aliyu Sokoto ya jagoranta, ta amince da bayar da katin shaida ga ɗaliban makarantun sakandaren gwamnati. 
Haka majalisar ta amince a yi gyaran fuska ga dokar da ta samar da hukumar Zakkah da waƙafi ta jiha.