Mutum Biyu Sun Mutu Wasu 10 Na Fama Da Cutar  Amai Da Gudawa a jihar Adamawa

Mutum Biyu Sun Mutu Wasu 10 Na Fama Da Cutar  Amai Da Gudawa a jihar Adamawa

  

Daga Ukasha Ibrahim.

Annabar cutar amai da gudawa wanda akafi sani da Cholera" ta 'bullo a jihar Adamawa inda tuni ta hallaka mutane biyu har lahira 

A Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta jihar Adamawa tafitar jiya a karkashin jagorancin Dr . Celine Laori ta ce cutar ta mamaye kananan hukumomi har hudu a jihar sannan yakara da cewa izuwa yanzu mutane goma sha daya ne 11 suka kamu da cutar inda tuni cutar ta hallaka mutane a karamar hukumar Guyuk da Shelleng wanda ke kudancin jihar, acewar jaridar Yola 24 

Kwamishinar ta kara dacewa , gwamnatin jihar Adamawa tana nan tana bincike  a duka kananan hukumomi 21 da suke jihar koda za a samu bullar cutar awasu wuraren  sanan ta kara dacewa gwamnati nayin duk iya bakin kokarinta wurin ganin ta samar  da dukkan wata gudumawa  bayan bullar wanan cutar awasu wurare acikin jihar 

A karshe ta 'kirayi mutane da su kasance masu kula da tsaftan  muhallinsu abincin su ,abincin su da kuma ruwan shan su domin kaucewa daga kamuwa da wanan cuta ta amai da gudawa