Gwamnan Bauchi  Ya Rabawa Manyan Sakatarori Sabbi Motoci Don Ƙarfafa Musu

Gwamnan Bauchi  Ya Rabawa Manyan Sakatarori Sabbi Motoci Don Ƙarfafa Musu

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya raba sabbin motoci ga sabbin manyan sakatarorin ma'aikatu da hukumomin gwamnati da gamayyar ƙungiyoyin kwadago.

Da yake jawabi yayin bikin miƙa motocin a fadar gwamnati, Bala Muhammad yayi kira ga manyan jami'an gwamnatin da su duƙufa wajen sauke nauyin dake kan su ta hanyar sadaukar da kai kana yace gwamnatin sa ta shirya tsaf don biyan basukan kuɗaɗen fanco da ratuti da ta gada daga gwamnatocin da suka gabata don haɓaka tattalin arzikin al'umar jiha.

Ya ƙara da cewa yana sane da halin da ɗumbin matasan da suka kammala manyan makaranti da jami'oi inda ya ƙara da cewa akwai shiri na musamman na ɗaukar su aiki a ma'aikatu da ofisoshin gwamnati.

Da yake yabawa sakatarorin kan marawa gwamnatinsa baya kuwa, Muhammad yace za'a miƙa sauran motocin ga ma'aikatu don sauƙaƙa gudanar da aikin gwamnati.

Ya yabawa ƙungiyoyin kwadago inda yace za'a ba su motocin ne sakamakon nagartacciyar alaƙar aiki tsakanin su gwamnati da kuma ƙara musu azamar aiki.

Ya faɗawa mahalarta bikin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da samar wa al'umar jihar Bauchi kayan more rayuwa da romon dimokraɗiyya inda ya ƙara da cewa an samu nasarar yiwa sakatariyar Abubakar Umar kwaskwarima karo na farko tun bayan gina ta shekaru talatin da suka shuɗe.

Gwamna Bala sai yayi kira ga ma'aikatan gwamnati da su kula da gine-gine ofisoshin sakatariya a dukkanin ƙananan hukumomi ashirin da aka yiwa kwaskwarima kana yace za'a samar musu da kujeru da sauran kayan aiki baya ga samar da motoci wa daraktocin ma'aikatu.

Tun farko da yake jawabi a madadin manyan sakatarotin, shugaban ma'aikata na jiha Alhaji Yahuza Adamu Haruna yabawa Gwamna Bala kan ayyukan sa a sashen kiwon lafiya, hanyoyi, ilimi, tsaro da sauran su duk da ƙarancin kuɗaɗe da ƙalubalen tattalin arziki.

Yahuza Haruna sai ya kirayi ma'aikata da su marawa gwamnatin baya don cigaba da samun romon dimokraɗiyya.