'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50 a Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50 a Sakkwato

Mahara sun sace kusan mutum 50 da suka tafi Sakkwato wurin daurin aure suna kan hanyarsu ta komawa Zamfara barayin suka dirar masu.

Shaidu sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a Yammacin ranar Asabar, a lokacin da mutanen ’yan Jihar Zamfara ke kokarin komawa gida Gusau bayan halartar wani daurin aure a garin Tambuwal.

A zantawarsa da manema labarai, Shugaban Karamar Hukumar Tureta, Abubakar Salihu, ya ce ’yan bindigar sun yi nasarar kwasar mutanen a tsakanin Karamar Hukumar ta Tureta da ke Jihar Sakkwato da Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun bude wuta akan daya daga cikin ayarin motocin matafiyan, abinda ya tilasta musu tsayawa, inda suka kwashe matafiyan suka gudu da su cikin daji.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce a halin yanzu jami’ansu da sauran jami’an hadin gwiwa na gudanar da bincike domin gano sauran wadanda ke hannun ’yan bindigar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, akasarin matafiyan da aka sace masu sana’ar sayar da wayoyin sadarwa ne a kasuwar Bebeji Plaza da ke Jihar Zamfara.

Aminiya ta ruwaito cewa, 20 daga cikin mutanen da aka sace sun kubuta amma sauran 30 din an yi awon gaba da su zuwa daji.

Shugaban masu sanaar sayar da waya reshen Jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Garba Mukhtar ya ce ’yan bindigar sun yi amfani da wayar salula ta daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su wajen kira inda suka sanar cewa mambobinsu 30 na tare da su.

Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya dai na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga wadanda ke kashe matafiya da mazauna karkara tare da garkuwa da wasu domin karbar kudin fansa.

A kwanan baya lamarin ya yi sauki kafin daga baya lamarin ya kazance musamman kan hanyar Sakkwato zuwa Zamfara.