Gwamnatin Yobe Ta Gyara Gadar-Katarko Wadda Ambaliyar Ruwa Ya Ruguza

Gwamnatin Yobe Ta Gyara Gadar-Katarko Wadda Ambaliyar Ruwa Ya Ruguza
 

Daga Muhammad Shamsudeen, Yobe.

 

Bayan sama da kwanaki uku ta na aiki tukuru, injiniyoyi a Ma’aikatar Ayyuka ta Yobe sun yi nasarar gyara Gadar Katarko, wadda ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da ita a daren Lahadi, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jama'a a jihar.

 
Wakilinmu ya rawaito cewa, Gadar Katarko wadda a shekarar 2014 mayakan Boko Haram suka jefa wa bam wanda hakan ya jawo katsewar babbar hanyar, wanda kuma ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Lahadin da ta gabata ya sake ruguzata.
 
Har wala yau, Gadar-Katarko tana daya daga cikin manyan gadoji da suka hada kananan hukumomin biyu da rikicin Boko Haram ya fi shafa (Gujba da Gulani) a jihar Yobe, wadda kuma ta hada jihar Yobe da kudancin jihar Borno, jihar Gombe, Taraba da Adamawa.
 
Gamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ziyarci wannan gada a ranar Talata, inda ya jajanta wa al’ummar yankin kan bala’in ambaliyar ruwar da ya jawo katsewar gadar tare da jawo mummunan asara a yankin.
 
Gwamna Buni ya umurci Ma’aikatar Ayyuka ta gaggauta gyara gadar saboda mahimmancin da take dashi a fannin bunkasa tattalin arziki ga al’ummar jihar da ma jihohin da ke makwabtaka da ita.
 
“Ku yi iya kokarinku wajen ganin an sake hada wannan hanyar don amfanin al'ummar wannan yanki cikin hanzari."
 
“Hanyar Katarko da ta hada jihohin Yobe da Borno da sauran jihohin da ke makwabtaka da ita na da matukar muhimmanci a gare mu musamman, sake gyara gadar cikin hanzari zai taimaka musamman wajen inganta harkar tsaro a jihar.” inji Gwamnan.
 
A nashi bangaren, Daraktan Injiniyoyi a Ma’aikatar Ayyukan jihar Yobe, Engr. Usman Ahmed ya sanar da cewa ma’aikatar ta yi aiki tukuru na ba dare ba rana domin aiwatar da umarnin da gwamnan ya bai wa Ma'aikatar tare da kokarin ganin an sake gyara gadar don ci gaba da amfani da ita kamar yadda aka saba.