'Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sokoto

'Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sokoto

'Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato 

 
 
'Yan bindiga sun shiga garin Chaco a ƙaramar hukumar Wurno ta jihar Sakkwato cikin daren Assabar  in da suka yi garkuwa da amarya da aka shata ɗaura aurenta a wannan Lahadi tare da ƙwayenta su 14 dake kwance ɗaki ɗaya.
Ana cikin shagalin buki ne 'yan bindigar suka mayar da murna baƙin ciki.
'Yan bindigar sun shigo garin a kafa suka tafi gidansu amarya kai tsaye ba tare da sun taɓa kowa ba.
Aminiya ta ji ta bakin ɗaya daga cikin mahaifan ƙwayen Amarya kan lamarin ya ce wasu na cewa yaran su 15 ne wasu na faɗin su 13 ne har amarya 'yan bindigar suka tafi da su har da  ɗiyata tana cikinsu.
"Kuma 'yar tawa 'yar uwar amarya ce ta zo ne domin yin bukinta anan Chaco, ban yi tsammanin nan za ta kwana ba, ashe rabon wannan ƙaddara ya cika da ita ne.
"A bayanin da muka samu 'yan bindigar sun shigo garin ba ta in da suka saba shiga ba da misalin ƙarfe 12 na daren Assabar ba tare da yin halbi ba kuma a ƙafa, kai tsaye suka yi gidan su Amarya suka shiga ɗakin da take da mutanenta, suka tafi da su a lokcin da za su bar garin ne matasa masu sintiri suka ɗan yi musayar wuta da su, har suka harbi ɗan sintiri guda ga hannu, a haka suka bar ƙauyen tare da matan su 15," a cewarsa.
Ya ƙara da faɗin 'yan bindigar har yanzu ba su kira kan abin da suke buƙata ba.
Ya ce awa ɗaya da rabi bayan tafiyar 'yan bindiga, jami'an tsaro sun zo har in da aka sace yaran.
Da ba a ɗauki yarinyar ba yau(Lahadi) ne za a ɗaura aurenta a kai ta gidan mijinta.
Lamarin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a yankin gabascin Sakkwato.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Sakkwato Ahmad Rufa'i bai ɗaga wayar waƙilinmu ba a lokacin da ya kira shi, don jin hoɓɓasar jami'ansu kan lamarin.