Gwamna Fubara ya faɗi kalmomi masu ratsa zukata ga mutanensa

Gwamna Fubara ya faɗi kalmomi masu ratsa zukata ga mutanensa

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya dawo Fatakwal ranar Juma’a bayan watanni shida da aka dakatar da mulkinsa sakamakon dokar ta-baci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a ranar 18 ga Maris 2025.

Fubara ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Fatakwal da misalin ƙarfe 11:50 na safe, inda dubban magoya baya suka taru domin tarbar sa. 

Sai dai bai bayyana a gidan gwamnati ba duk da taron jama’a da suka jira shi.

Tun bayan hawan sa mulki a 2023, Fubara ya samu sabani da wanda ya gada, Ministan Abuja Nyesom Wike, rikicin da ya raba majalisar dokokin jihar gida biyu. Lamarin ya sa Tinubu ya nada tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Admiral Ibok-Ete Ibas (rtd.), a matsayin mai rikon gwamnati.

Ibas ya mika mulki ranar Laraba, inda ya bukaci ’yan siyasar jihar da su rungumi tattaunawa da mutunta juna.