Kisan Sarkin Gobir: Kungiya Ta Nemi Gwamnan Sakkwato ya yi abu uku ko ta maka shi kotun Duniya

Kisan Sarkin Gobir: Kungiya Ta Nemi Gwamnan Sakkwato ya yi abu uku ko ta maka shi kotun Duniya

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Afrika ta nemi Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto da ya yi wasu abubuwa uku ko ta kai shi kotu domin tana ganain sakacinsu ne ya sa Sarkin Gobir ya rasa ransa hannun ‘yan bindiga a satin da ya gabata.

A wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani  wanda Dakta Suleiman Shu'aibu Shinkafi yake magana amadadin kungiyoyin kare hakin dan adam na Afrika ya ce "matsayarmu bayan mun yi taro kungiyoyinmu kusan 18 sun yi alawadai da kisan da aka yi wa basarake Sarkin Gobir na Sabon Birni, mun daura laifukan gaba daya kan gwamnatin jihar Sakkwato don ita ke da hakkin kare Basaraken, amma 'yan bindiga suka kama shi tsawon sati uku har ya mutu sun yi sakaci da aikinsu.

"Muna da bukatu har guda uku da muke son gwamnatin Sakkwato ta aiwatar, na farko muna kira ga gwamnatin  Sakkwato ta yi gaggawar korar kwamishinan tsaron jiha, na biyu muna son a biya diya ga iyalan margayi Sarkin Gobir, sai na uku  gwamnati ta yi jawabi na kwantar da hankali  ga 'yan Nijeriya da mutanen Sakkwato da Gobirawa duk in da suke kan wannan ibtila'i da ya same mu," a cewarsa.

Haka ma Dakta a jawabin nasa ya ce in gwamnati ba ta yi haka ba sun bayar da sati biyu za su kai ta kotun ICC domin fuskantar shari'a.