Gwamnati ta dakatar da Shugabannin Sakandare 6 a Sakkwato 

Gwamnati ta dakatar da Shugabannin Sakandare 6 a Sakkwato 
Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin Gwamna Ahmad Aliyu ta dakatar da Shugabannin makarantar sakandare guda shida kan aikata laifin zamba cikin aminci na karbar kudi hanun dalibai da walakanta shugabanni.
Kwamishinan ma'aikatar ilmin Firamare da sakandare na jiha Farfesa Ahmad Ladan Ala ya aminta da dakatar da Shugabannin makarantun guda shida Saboda sun karbi kudin sakamakon jarabawa hannun dalibbai da suka kammala karamar sikandare(JSS) ba tare da izinin gwamnati ba, wasu daga cikinsu sun walaƙanta shugabanni dake sama da su.
Shugabannin da aka dakatar sun hada da "shugabar makarantar mata ta Nana da Makarantar gwamnati ta Gagi(GDSS) da makarantar sakandare ta Mana da Kwalejin Giginya da Baizik ta Mana, da Sikandaren Silame.
Kwamishina da yake bayani kan saba dokar da aka yi ya kafa kwamiti na mutum biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Namakka Tukur don su duba zarge-zargen da aka yi masu da ya sa aka dakatar da su.
Kwamishina a bayanin da jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar Ibrahim Muhammad Iya ya fitar ya umarci shugabannin su mika ragamar makarantun ga hannun mataimakansu na mulki nan take.
"Ma'aikatar ilmi za ta cigaba da yin tsayin daka ta tabbatar da tarbiya da rike amana da gaskiya a dukkan makarantun jihar Sakkwato," a cewarsa