Gidauniyar Aurar Da Marayu Da Matasa Ta Jihar Bauchi Na Neman Ɗaukin Gwamnati Da Masu Hali
Daga Aminu Abdullahi Gusau
Anyi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta jihar Bauchi da su taimaka wa Gidauniyar aurar da marayu da matasa domin su ci gaba aurar da marayu da kuma matasa wayan da basu da halin yin aure.
Shugabar wannan gidauniyyar malama Ummu Kalsum ce tayi wannan kiran a lokacin da take zantawa da manema labarai, inda tace hakika akwai marayu da dama wayanda yanzu haka sun isa aure amma babu halin aurat dasu.
Tace yanzu haka inda suka bude ofishin su an karbe shi, saboda na magada ne, a don haka suna bukatar ofis da kuma kayan koyar da yaran ayukkan da zasu dogaro da kansu.
Shugabar ta ce a halin yanzu sun aurar da marayu kusan su goma sha shidda, haka ma matasa su hudu, kuma su suka samar masu da kayan Daki da duk abunda ake bukata.
Daga nan ta jawo hankalin gwamnatin jihar Bauchi da cewa su saka wannan shirin da wannan gidauniya keyi cikin shirye shiryen da suke yi na tallafawa marayu.
Malama Ummu Kalsum tace, babban dalilin da yasa suka kafa wannan gidauniyar shine domin rage zunace zinace tsakanin matasa, da kuma dogaro da kansu.
"Na samu kwarin gwiwar yin wannan gidauniyar ne daga mijina wanda yake tallafa mini wajen ganin mun aurar da marayun da matasan da basuda halin yin aure a fadin jihar Bauchi da kewaye.
" Yanzu dai muna bukatar gwamnati ko masu hannu da shuni dasu tallafawa wannan gidauniyar da fili domin mu gina ofis, da kuma kayan aiki domin yanzu haka akwai marayun dake gidana ina koya masu sana'ar hannu domin su dogara da kansu.
"Kunga idan mun samu taimakon kayan aiki sai mu kara yawan yaran da zamu koya wa sana'a da fatar Allah yasa wayan da akayi wannan kiran don su dasu taimaka."inji Ummul kalsum.
managarciya