Uwar Gidan Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki Ta Ƙaddamar Da Bada Tallafi Ga Mata A Kebbi

Uwar Gidan Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki Ta Ƙaddamar Da Bada Tallafi Ga Mata A Kebbi

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Uwar gidan mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar kebbi Hajiya Uwani Usman Mohammed Ankwe dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Zuru, a majalisar jihar kebbi, 

Hajiya Uwani Usman Mohammed Ankwe ta kaddamar da rabon bada jari na kudi ga mata domin dogaro dakai, Uwani ta bada wannan tallafin ne ga mata domin su samu abin dogaro dakai, 

Kamar yadda uwar gidan Hon Usman Mohammed Ankwe ta tsara na samar da wannan tsari na tallafawa mata da zai rage musu radadin talauci da kawar da rashin aikin yi a fadin Zuru baki daya, 

Yana daga cikin cikar burin Hajiya Uwani Usman Mohammed Ankwe taga al'ummar Zuru musamman mata daya daga cikin cibiyoyin habbakar Kasuwanci, 

Haka m acikin jawabin ta Hajiya Uwani ta yabawa mai gidan ta Hon Usman Mohammed Ankwe bisa kokarin da yake yiwa al'umma wajen ganin ya kyautatawa musu da abubuwan more rayuwa, 

Sannan Hajiya Uwani tayi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar daya dace dan kwao cigaba mai dorewa a yankunan mu baki daya,

Cikin jawabin masu ruwa da tsaki the kaddamar da tallafin mata acikin garin Zuru Kansilan Dabai Hon Hadiza tayi godiya da jinjina ga Uwar gidan Hon Usman Mohammed Ankwe bisa dunbin alkhairi da taki yiwa mata a wannan yankin namu kana kuma tayi addu'a Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Abbakar Aleeyu Anache