NA SO MU YI SULHU TUN FARKO DOMIN KULA DA LAFIYAR FATIMA DA SAMAR MATA MAFITA, AMMA ABIN YACITURA DOMIN IYAYEN TA BA SU BA DA HADIN KAI BA
Mamar Aliyu ta nemi Dangin Fatima su yafe ma Aliyu.
Wata ɗaya da samun rahoton Yanke kafar Ɗaliba Fatima a lokacin Murnar Kammala jarabawar NECO ga ɗalibban makarantar Kalipha International Secondary School Ajahar Sokoto, an lashe wata ɗaya cif ana kai ruwa rana tsakanin dangin Fatima da dangin Aliyu wanda ya bige Fatima har Saida aka yanke ƙafarta.
Rahoton da muka samu daga muryar mamar Fatima Hajiya Hadiza, ta bayyana cewa babu Maganar yafiya. Koda Sama da kasa za su haɗe ba za su yafe ba sai an biya su Diyyar ƙafar Fatima. "Kuɗi Sunci Bura'ubansu"
Afirar da Muka yi da Mai baiwa Gomna Tambuwal shawara a kan Hakkin Bil'adama Hajiya Ubaida Bello, ta shaida mana cewa a chikin zaman Sulhu da muka yi da Iyayen Fatima, Iyayen Aliyu da Jami'ai na Human Rights, mun tashi babu daɗin rai. domin Mahaifin Fatima ya gaya muna maganganu marasa dadi a idon mu. Ya kuma tabbatar muna da cewa shi ba zai sulhunta da kowa ba sai dai a biya shi diyyar kafar 'yar shi da kuma diyyar ɓacin ran ta na har iyakar rayuwar ta.
Alokacin da Muka yi zama da Mamar Yaron tare da Ma'aikatan gidan Jaridu Jiya Narba, Mahaifiyar cikin Muryar tausayi ta shaida mana cewa sun bi duk hanyar da za'abi wurin ganin an samu sulhu tsakanin su da dangin Fatima tun farkon lokacin da abun ya faru zuwa yanzu, amma dangin Fatima ba su aminta a yi Sulhun ba.
Mun ba da duk abin da ake bukata ga lafiyar Fatima ba tare da kasawa Ko gajiyawa ba, amma iyayen bas u hakura ba. Mun shaida musu mun ɗauki nauyin komai na Jinyar Fatima har zuwa samun Sauki da Yi mata kafar roba amma basu haqura ba. A duk Lokachin da naje asibiti domin duba Fatima hantara ta ake yi na rasa bacci da cin abinci saboda yanayin Fatima inji Mamar Aliyu.
Mamar ta kara da cewa tafi tausayin yanayin Fatima da'aka yankewa qafa take fama da jinya asibiti fiye da Ɗanta Aliyu dake zaman gidan kaso tsawon wata ɗaya Ahalin yanzu...
Adaidai Lokacin da wasu ke tausaya wa Fatima, wasu Mutanen ma suna tausayawa Aliyu zaman shi karamin yaro a kurkuku chikin barayi da masu laifin garkuwa da mutane da Mashaya da Mahaukata da Mutane Masu hatsarin gaske. Har wasu ke gudun kar zamansa gidan kaso ya zama Silar sauyawar rayuwar sa zuwa wani Mutum na daban achikin al'umma.
Mamar Aliyu ta rufe Magana Cikin kuka da zubda hawaye tana cewa wannan kaddara che daga Allah muna roqon a yi haquri a yafe mana!