Dalilin Da Ya Sa Wani Matashi Ya Rataye Kansa a Jihar Kano

Dalilin Da Ya Sa Wani Matashi Ya Rataye Kansa a Jihar Kano
Gwamna Ganduje
 
Wani matashi ya hallaka kansa ta hanyar rataya a ƙaramar hukumar Kiru ta jihar kano.
Matashin ɗan kimanin shekarau 30 da ba a bayyana sunanan sa ba, ya rataye kansa ne a ranar Talatar da ta gabata.
Wani ganau ya shaidawa majiyar mu cewa matashin ya rataye kansa ne a wata bishiya dake gonar wani mutum, daga nan ne bayan mai gonar ya ganshi rataye a bishiyar sai ya sanarwar da ofishin ƴan sanda.
Daga bisani jami’an ƴan sanda suka isa wurin suka sauko da shi suka garzaya dashi Asibitin ƙwararru na Murtala da ke Kano.
Sai dai bayan da Likitoci suka duba shi ne suka tabbatar da ya mutu.
Kazalika rundunar ƴan sanda ta ƙasa shiyyar Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin a ta  bakin kakakin rundunar ƴan sanda DSP Abdullahi Hauruna Kiyawa.
Kiyawa yace izuwa yanzu ba su gano musabbabin da yasa ya rataye kansa ba. Sannan ya tabbatar da cewa har yanzu marigayin na Asibitin, ƴan uwansa ba suje sun ɗauki gawarsa ba.