Wadanda Ke Son A Fitar Dan Takarar Shugaban Kasa Ta Hanyar Sulhu Ba Su Da Gaskiya---Wike

Wadanda Ke Son A Fitar Dan Takarar Shugaban Kasa Ta Hanyar Sulhu Ba Su Da Gaskiya---Wike

Gwamnan Rivers Nyesome Wike ya ce wadanda ke son a fitar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP ta hanyar sulhu ba su da gaskiya.

Gwamnan wanda ke son PDP ta tsayar da shi a zaben 2023 ya ce duk wanda ya samu nasarar zama dan takara a jam'iyarsu zai mara masa baya.

Wike ya ziyarci jihar Neja domin neman goyon bayansu a zaben fitar da gwani da za a yi a 29 ga watan Mayu, ya ce yana aminta da silhu in an sanya adalci da gaskiya da baiwa kowa hakkinsa.

"Muna aminta da silhu in akwai gaskiya da adalci amma wadanda kemagana kan silhu ba su da gaskiya, kuma ba maganar silhu a tsarin dokokin jam'iya."