Sarkin Gaya Ya Karɓi Sandar Mulki
Daga Musa Dahiru Ajingi Kano
Manyan mutane a jiya Assabar sun haɗu a garin Gaya wurin baiwa sarki Aliyu Ibrahim Gaya(Karimau mai Gabas) sandar .
Sabon Sarkin ya gadi mahaifinsa Ibrahim Abdulkadir wanda ya rasu a 22 ga Satumbar shekarar data gabata yana da shekara 91.
Naɗin ya biyo bayan amincewar da masu nada sarki a fadar suka yi in da gwamnati ta aminta a naɗa sabon sarkin.
Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya taya sarkin Gaya murna ya roki samun zama lafiya ga ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya roƙi sarkin kar ya bari martabar sarautar ta faɗi ya riƙe girman gidan.
Ya ce gwamnatinsa za ta bayar da goyon baya ga duk abin da zai ɗaga martabar sarautar.
managarciya