Matsalar Tsaron Nijeriya Za Ta Zama Tarihi------Sanata Wamakko
Sanata Wamakko ya bayyana cewa a satin da ya gabata sun tattauna kan yadda za a kawo karshen wannan matsalar da ta addabi sassan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Wamakko ya ce daukar mataki kan lamarin tsaro ba abu ne da za a fito Fili a fadawa Jama'a irin matakin da ake dauka ba, lura da cewa su kan su maharan suna da wakilai a ko'ina kuma a shirye suke su dauki na su matakin domin kaucewa Wanda gwamnatin ke dauka. Saboda haka ya bayyana cewa ba za a bayyana irin wadannan matakan ba, sai dai ya ba da tabbacin cewa nan bada jimawa za a zo karshen matsalar da yardar Allah.
Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa ta Nijeiriya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto ya ba da tabbacin cewa nan bada jimawa ba gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kawo karshen matslar tsaron da ake fama da ita.
Sanata Wamakko ya fadi hakan a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi na Mintuna Talatin a Gidan Talabijin na TTV ( Tambarin Hausa TV), Wanda aka nuna yau Larba.
Sanata Wamakko ya bayyana cewa a satin da ya gabata sun tattauna kan yadda za a kawo karshen wannan matsalar da ta addabi sassan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Wamakko ya ce daukar mataki kan lamarin tsaro ba abu ne da za a fito Fili a fadawa Jama'a irin matakin da ake dauka ba, lura da cewa su kan su maharan suna da wakilai a ko'ina kuma a shirye suke su dauki na su matakin domin kaucewa Wanda gwamnatin ke dauka.
Saboda haka ya bayyana cewa ba za a bayyana irin wadannan matakan ba, sai dai ya ba da tabbacin cewa nan bada jimawa za a zo karshen matsalar da yardar Allah.
Ya gabatar da bukatar ci gaba da yin addu'o'i ga 'yan kasa domin neman taimakon Allah ga kawo karshen wannan lamari.
managarciya