Dubun Wata Mata Mai Sayen Abinci Da Jabun Kuɗi Ya Cika

Dubun Wata Mata Mai Sayen Abinci Da Jabun Kuɗi Ya Cika


'Yan sanda sun kama wata mata da ake zargi da sayen kayan abinci da jabun kuɗi a kasuwar Oregbeni cikin Benin City jihar Edo.
An samu wadda ake tuhumar da kaya da suka wuce dubu 200 tare da jabun kuɗi na naira 1000.
Ɗaya daga cikin 'yan tireda ne ta yi ƙarar wadda ake zargi bayan ta ba ta jabun kuɗi shi ne ta an karar da jama'a.
Bayan an gano mai laifin bayan tana ta faɗi tashin zuwa shaguna don sayayya.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda SP Chidi Nwabuzor ya ce har yanzu bai san komai kan lamarin ba.