Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Zuru Ya Nuna Gamsuwarsa Ga Kwamitin Cigaban Yankinsa

Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Zuru Ya Nuna Gamsuwarsa Ga Kwamitin Cigaban Yankinsa

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Zababben shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru, Honarabul Bala Mohammed Isah Gajere ya halarci taron masu ruwa da tsaki a fannin ilimin zamani da zaman takewar dan adam acikin garin Zuru.

 

A yayin jawabin sa Hon Bala Mohammed Isah Gajere, yayi amfani da wannan damar wajen kira ga daukacin al'ummar kasar Zuru, dasu cigaba da marawa wannan kwamitin baya kana yace an kafa wannan kwamitin ne domin yadda zasu rika zakulo ayyuka da bada fifiko ta fannin ilimin zamani, da kuma tabbatar da matasa sun samu ingantancen rayuwa, 
ont-size: large;"> 
A cewar sa Hon Bala Mohammed Isah Gajere, ya kara da cewa wannan kwamitin da aka shirya tare da lalabo hanyoyi na kawar da talauci da fifita muhimmancin ilimi
 
Kuma Gajere yayi kira ga kungiyoyin matasa da su yi aiki tare da wannan kwamitin domin Inganta rayuwar matasa da sama musu aikin yi domin dogaro dakai, 
 

Yadda aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a karamar hukumar mulki ta Zuru dake jihar kebbi, wannan taron ya samu halartar manyan yan siyasa kuma da manyan malaman jami'oi hadi da sarakunan gargajiya, ya sami goyon bayan tsofaffin Sojoji, 

 
Gajere ya nuna gamsuwa dangane da yadda wannan taron ya gudana domin karawa juna sani a fannin ilimi da tarbiyya da nuna amintaka da yadda za'a shawo kan matsalolin dake addabar al'umma musamman a bangaren ilimi da bada fifiko da hanyoyi domin lalabo hanyar kawo cigaba da habbaka ilimin zamani, 
 
Da yake jawabi a wurin taron shugaban wannan kwamitin farfesa A,D Isha ya yabawa mai martaba sarkin Zuru, da shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru bisa ga gudunmuwa da goyon bayan da suka bamu wajen shirya taron tare da jan hankalin matasa da suka halarci taron wajen ganin sun yi anfani da taron wajen kulla alaka da hulda a tsakanin al'umma, 
 
Taron masu ruwa da tsakin ya samu halartar manyan malaman jami'oi,  farfesa S,D Manga Education, Dr Thomas Gode Health Mr, Bamaiyi An'iko Dabai Infrastructure, kuma ya samu halartar sarkin Sakaba da Sarkin Danko da wakilin Sarkin Fakai,
 
A nasa jawabin wakilin mai martaba sarkin Zuru  His Royal Highness, Maj, General, Dr Muhammad Sani Sami Con, mni (LLD FICEN,) Sami Gomo II, the Emir Of Zuru, a lokacin da yake bayyana farin cikinsa a wannan taron Sarkin wasagu ya nuna farin cikinsa game da kafa wannan kwamitin da manyan malaman jami'oi suka yi domin farfado da martabar wannan yankin namu, 
 
Ya cigaba da cewa mai martaba sarkin Zuru ya nuna goyon bayansa sosai da kuma duk wani yunkuri da zai dawo da ka'idoji da martabar matasa a wannan zamani,