'Yan-Sa-Kai Sun Kashe Fulani 11 bayan Harin Da 'Yan Bindiga A Sakkwato
Hudu daga cikin Fulanin sun samu mummunan raunuka a kan harbin da an ka yi masu, suna karbar magani a asibitin kashi ta Wamakko.
Akalla fulani 11 ne 'yan sa kai da aka fi sani da 'yan banga suka kashe a kasuwar kauyen Mammande a karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sakkwato.
Hudu daga cikin Fulanin sun samu mummunan raunuka a kan harbin da an ka yi masu, suna karɓar magani a asibitin kashi ta Wamakko.
Shugaban ƙaramar hukumar Gwadabawa ya tabbatarwa manema labarai lamarin ya ce 'yan-sa-kan sun zo ne daga makwabtansu a Goronyo amma dai bai tabbata ba ko a garin suke ko akasin haka.
A cewarsa Fulanin sun zo daga makwabtan kauyukkansu suka zo kasuwar domin sayen kayan abinci da sauransu.
Aya ya bayyana lamarin matsayin wanda ya zo ba za ta, 'yan sa kai sun bindige fulani 15 kai tsaye da bindigar toka harba ka tsere.
Ya ce lamarin ya faru da karfe uku na ranar Alhamis a lokacin da kasuwar ta cika take ci masaya da masu sayarwa na ta hadahada.
"Sha ɗaya daga cikinsu suka mutu nan take, hudu suka samu munanan raunuka a hannu a wurin kare harbin bindiga da aka yi masu.
"A maganar da nake yi da kai, mun kai wadanda suka samu rauni a adibitin kashi ta Wamakko, gawarwakin kuma mun kai su dakin ajiye matattu na jiha",a cewar Shugaban karamar hukuma.
Ya ce an kasa kama wadanda suka yi aikin saboda makaman da ke rike da su. Gwamnatin jiha ta soke aiyukkan sa kai saboda wuce wuri da daukar doka a hannunsu.
Matattun an kai su ne a asibitin kwararru ta jihar Sakkwato.
Ɗaya daga cikin fulani a jihar Sakkwato da ya yi magana da wakilinmu ya kira wannan aikin jahilci ne da rashin yakamata.
Har yanzu ba a san dalilin wannan harin ba amma wasu na danganta shi da yawan harin 'yan bindiga da ake samu a jihar 'yan fashin dajin ana ganin mafi yawansu fulani ne.
Duk yunkurin jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ASP Sanusi Abubakar bai yi nasara ba.
managarciya