An ga watan Ramadan a Nijeriya----Sarkin musulmi

An ga watan Ramadan a Nijeriya----Sarkin musulmi
Mai martaba Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan a yau Lahadi abin da ke nufin za a tashi da Azumin Ramadan a gobe Litinin.
Sarkin musulmi a fadarsa bai zayyano wuraren da aka ga watan ba sai dai ya ce ya ce "yau Lahadi 29 ga  watan  Sha'aban hijira 1445 daidai da 10 ga watan Maris 2024 an kawo karshen watan Sha'aban.
"Mun samu labarin ganin watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci wurare da yawa a kasar nan kuma kwamitocin ganin wata sun tantance sahihancin bayanan, bisa ga haka mun amince gobe Litinin 11 ga Maris ta zama daya ga watan Ramadan,"a cewar Sarkin Musulmi.
Ya yi kira ga Musulmi su yawaita addu'o'i a Watan Ramadan.
Ya kuma nemi masu kudi a cikin al'umma da su taimaki talakkawa da gajiyayyu a lokacin ibadar azumin Ramadana musamman abinci da sauran abubuwan bukata don rage wahalar da ake ciki ta tsananin rayuwa da ake fuskanta a Nijeriya.