Zaɓen Ƙananan Hukumomi Zai Koma Hannun Hukumar INEC —Majalisar Waƙillai

Zaɓen Ƙananan Hukumomi Zai Koma Hannun Hukumar INEC —Majalisar Waƙillai

Daga Shamsudeen M Sani Yakaji.

Biyo bayan hukuncin kotun ƙolin a ranar Alhamis da ta gabata, ta yiyu yan majalisa su yi wa kundin tsarin mulkin mu kwaskwarima yadda zaɓen ƙananan hukumomi zai dawo hannun INEC.

Yayin wani taron manema labarai, Sanata Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta Kudu yace, za su tabbatar gwamnoni sun yi biyayya ga hukuncin kotun. Sannan suma za suyi iya ƙoƙarin wajen yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don ganin hakan ya tabbata.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanata dake wakiltar Delta ta kudu, ya bayyana cewa dole su yi wa kundin tsarin mulkin gyara domin a ba Hukumar INEC ragamar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin.

Yace dole a ba mutane dama su rinƙa zaɓen wanda suke so. Ba kamar abun da ke faruwa ba yanzu. Ya bayyana zaɓen ƙananan hukumomi da akayi a Delta satin da ya gabata a matsayin wasan kwaikwayo ne kawai