Day One: @RamadanKareem: Yadda Za Ki Hada ƘOSAI Mai dadin Gaske
BASAKKWACE'Z KITCHEN
Day One:
ƘOSAI
INGREDIENTS
Kofi uku na wake
Albasa guda
Hanta
Ƙwai biyu ko baking powder
Tarugu da tattasai
Salt
Mangyaɗa
METHOD
Da farko aunty na zaki sami wake ki jiƙa shi da ruwa tsawon minti biyar ko goma sai ki tsameshi ki zuba a turmi ki surfa ,idan ya yi sai ki kwashe ki zuba a roba sannan ki zuba ruwa ki wanke shi ki cire duk wani datti dake cikinsa.
Idan kin gama sai ki ɗauko albasa, attaruhu, tattasai ki gyarasu sai ki zuba kan waken sannan ki markaɗa. ki samu ludayi ki bugashi sosai sannan ki kawo gishiri,ƙwai ko baking powder da dafaffiyar hantar ki da ki ka yanka ƙanana ki zuba sai ki ƙara juyawa,se ki ɗora kasko da mai kan wuta idan yayi zafi sai a ɗebo ƙullin ki da ludayi ki na zubawa cikin mai ɗin a hankali , sannan ki bar kowanne ɓangare ya soyu sai ki kwashe daga cikin mai ɗin a tsane shi a cikin kwando
MRS BASAKKWACE
managarciya