Dattawan Sakkwato Ta Gabas Sun Kafa Ƙungiyar Tallafawa Yankin 

Dattawan Sakkwato Ta Gabas Sun Kafa Ƙungiyar Tallafawa Yankin 
Dattawan Sakkwato Ta Gabas Sun Kafa Ƙungiyar Tallafawa Yankin 
Muhimman mutane daga yankin gabascin Sokoto sun jagoraci kafa  ƙungiyar tallafawa yankin SOKOTO EASTERN ZONE DEVELOPMENT ASSOCIATION (SEZDA)  da zimmar farfaɗowa  da tabarbarewar ilimin yara, kasuwanci, noma, da rashin aikin yi sakamakon hareharen ta’addanci da kinsan gilla da yankin yake fama dashi tsawon lokaci.
Ƙungiyar ba ta da wata alaka da siyasa ko jam’iyya an fito da ita ne domin taimakama yankin dake neman tarwatsewa sakamakon hareharen ta’addanci da garkuwa da mutane kan haka ne  muhimman mutanen da yakin yake da su, suka hada da manyan 'yan siyasa, Farfesoshi, doctoci na jami’a, ma’aikatan Gwamnati, tare da 'yan kasuwa suka hadu waje daya suka yi matsayar yin wannan kungiyar domin farfado da yankin.
Kamar yadda bayanin ya nuna kungiyar ba ta tsaya  yankin gabascin Sokoto kaɗai ba, ta shafi dukkan al’ummar jihar da suke son  taimakama yankin da duk abun da ya dace domin farfado da al’ummar da suka rasa ilimi, kasuwanci, da noma wanda har takai wasu daga cikin garuruwan kananan hukumomin da yankin yake das u sun gudu sun bar muhallansu, ba makarantu duk a rufe, ba kasuwanci, ba aikin noma sakamakon kisan gillar da ta’adanci da yankin yake fama da shi. 
Hakan ya kara sanya Dattawa da sarakunan gargajiyar yankin suka ga ya dace da sufito da wannan kungiyar domin ceto goben al’ummarsu daga taɓarɓarewa.
A bayanin an jero abubuwa guda huɗu da yankin yafi buƙata kamar:
1. Yankin Yana neman tallafin ta bangaren kudi domin gudanarda sha’anin rayuwar al’umma da suka rasa muhalansu da waɗanda ke cikin  talauci da rashin aikin yi.
2. Ana fama da matsalar abinci   yunwa ta tagaiyara jama'a da suka rasa yin noman abincin da za su ci balle sukai sauran kasuwa su sayar don sayen kayan masarufi.
3. Ana fama da matsalar rashin ilmin yaran mu da ba su makarantu, saboda ba kwanciyar hankalin da za’a nemi ilimi balle a gudanarda rayuwa.
4. Ana fama da karancin kayan tufafi dana kwanciya ga wadanda suke gudun hijira.
Akan hakane mukaga yadace da mufito da wannan kungiyar domin taimakon Al’ummarmu a matsayin mu na jagorori sai mu hada da taimakon da Gwamnati keyi Muna hakan zai sa Gwamnati taji dadin kara shigowa ta kamamuna.
Ita dai wannan kungiyar za’a kadamar da ita a karamar hukumar Gwadabawa a ranar Assabar 1st January, 2022
lokaci :- 10:00 Am
Kungiyar tanada manyan uwaye da jagorori da zasu halarta a wannan ranar.