Sama da gidaje dubu 50 ne suka samu naman layyar  wannan shekara a Sokoto-----Lawal Maidoki

Sama da gidaje dubu 50 ne suka samu naman layyar  wannan shekara a Sokoto-----Lawal Maidoki

Shugaban hukumar Zakka da wakafi a jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki ya sanar da jama'ar jiha nasarar da hukumar ta samu a naman layyar da ta rabawa mabuƙata domin ganin ta faranta masu a lokacin shagalin babbar  sallah a wannan shekara ta 2024.
Shugaban hukumar a wurin taron manema labarai da ya kira ofishin hukumar dake unguwar Tudun Wada ya ce bayan kammala rabon naman layyar ne yake sanar da jama'a hukumar Zakkah ce ta yi haɗin guiwa da wasu abokan tafiya dake ƙasar Turkiya waton Gidauniyar Erƙam da ƙungiyar tallafi ta Sulaimaniya.
"Gidauniyar ta yanke shanu 500, ta baiwa hukumar Zakka shanu 240, jihar Kebbi da Zamfara sun raba wanda aka ba su, mutane 6000 ne suka amfana da layyar.
"Ƙungiya ta so ta yanke shanu 2000, sai dai shanu 1,394 da Raƙumi 35 aka samu saboda wasu cikas da aka ci karo da su. An samar da wuri biyu domin yanka in da ofishin zakka 674  da IET 720, tsarin waɗan da suka amfana da naman Layyar sun haɗa da Masallatan Jumu'a, ƙungiyoyin addini dana sa-kai, hukumomin gwamnati, gundumomin iyayen ƙasa 87 dake jiha, cibiyoyin ciyarwa a watan Ramadan 134, ma'aikar lamurran addini ta jiha, makarantun Allo dake ƙarƙashin kulawar hukumar bayar da ilimin larabci ta jiha, Jami'an tsaro, marayu, gidajen gyaran hali da 'yan gudun hijira da kuma asibitoci."
Lawal Maidoki ya ce fiye da iyalai 50,000 ne suka amfana da sadakar naman layyar da aka raba a wannan shekara, ya godewa gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu da gwamnatinsa da majalisar Sarkin Musulmi da duk wanda ya ba da gudunmuwa aka samu nasarar wannan aikin.