SULTAN CHIPS

SULTAN CHIPS

MRS BASAKKWACE'Z KITCHEN GROUP






       SULTAN CHIPS


INGRIDIENTS:

Irish
Green bean
Carrot
Nama ko kaza
Ɗanɗano
Curry da kayan kamshi
Jajjagen tarugu
Lawashi
Mangyaɗa
Gishiri


YANDA ZAKI SARRAFA SHI

Da farko aunty na za ki fere dankalin turawan ki ko na hausa,de dai ruwa de dai tsaki, ki yanka yankan chips fale fale  kisa gishiri ki soya ya soyu, ki tafasa naman sa ko kaza ki yanka a tsaye kamar yankan chips, kin yanka carrot ɗinki haka da green beans ɗinki ma haka, ki yanka lawashi da ɗan tsawao kamar chips amma sirara. Ki soya kayan miya kamar cokali biyu,

sai kisa sauran ingredients ɗinki da kika yayyanka kisoyasu sama sama, sai kisa kayan ƙamshi da seasonings, ki jjuya ki zuba chips ki jujjuya, ki zuba ruwa tafashe kamar cokali biyar ki rufe kisa low heat ruwan ya tsotse.


MRSBASKKWACE