Kansila Ya Ginawa Mazabarsa Asibiti a Kebbi
Kansila a jihar Kebbi Ya Gina Katafariyar Asibiti Da Makarantar Zamani A Mazabar Shi.
Honarabul Moses G Dudu kansila ne a mazabar Rumu Daben Same a karamar hukumar Zuru dake jihar kebbi yayi amfani da kudin aljihunsa wajen gina wa al'ummar mazabar shi Katafariyar makaranta da asibiti.
Wannan shine Honabul Moses G Dudu kansila daya tilo da ya kafa tarihi kaf a cikin kansilolin jihar kebbi inda ya ware makuddan kudade domin gina wa jama'ar shi makaranta da asibiti domin samun saukin rayuwa.
Gina asibitin nada matukar muhimmanci ga mutanen yankin ganin yanda suke bukatar kiyon lafiya Mai iganci don kyautata rayuwarsu ta Tau da kullum.
managarciya