Gwamnan Sakkwato Ya Nada Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jiha

Gwamnan Sakkwato Ya Nada Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jiha

 

Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sakkwato ya nada wasu mukamai guda bakwai dake da muhimmanci.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Alhaji Abubakar Bawa ya sanyawa hannu ya ce gwamnan ya aminta da nada Alhaji Muhammad Bello Sifawa matsayin Sakataren gwamnatin jiha, in da Alhaji Aminu Dikko zai zama shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jiha.
Sauran mukaman sun hada da babban mataimaki na musamman kan gwamnati Barista Gandi Umar Muhammad, sai Alhaji Hussaini Gorau babban mataimaki  na musamman ga Gwamna, sai Bello Yahaya Wurno babban mataimaki na musamman kan huldar gwamnati da Faruk Labbo da Faruk Ahmad Shuni dukkansu an nada su mataimaka na musamman suma.